Majalisar dattijai a ranar Talata, ta ce kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL) ya bukaci karin lokaci don kare wasu tambayoyi 19 da suka shafi ɓatan dabon kuɗi sama da tiriliyan 210 a cikin bayanan kudaden sa na shekarar 2017-2023.
Bayanin hakan ya fito ne daga kwamitin majalisar dattijai mai kula da asusun gwamnati, wanda a watan Yuli ya baiwa shugaban kamfanin NNPCL, Injiniya Bayo Ojulari wa’adin makonni uku ya bayyana inda kudaden suka shiga.
Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala zaman, shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Wadada (Nasarawa ta Yamma), ya tabbatar da cewa kamfanin yanzu ya turo da sakonsa amma ya ce har yanzu kwamitin bai gama tantance sakon ba.