Shugaban kasar Zambia Hakainde Hichilema, ya ce daga matsayin dangantaka tsakanin kasarsa da Sin zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkanin fannoni a shekarar 2023, ya fara haifar da manyan nasarori.
Shugaba Hichilema ya bayyana hakan ne a jiya Laraba, yayin zantawarsa da wata tawaga ta wakilan kamfanonin Sin da na Zambia, inda ya godewa gwamnatin kasar Sin bisa daga matsayin dangantakar sassan biyu. Ya ce tuni Zambia ta fara ganin sakamakon hakan. Yana mai jaddada kyakkyawan sakamako da kasarsa ta samu, tun bayan da kamfanonin Sin suka fara nuna sha’awa da kafa rassansu a kasar.
Shugaban na Zambia ya kara da cewa kasarsa ta bude kofofinta na kasuwanci. Yana kuma fatan kamfanonin Sin za su fadada nazarin damammakin zuba jari da kasar ta samar. Ya ce Zambia na da tarin albarkatun kasa, tana kuma bukatar kudade, da fasahohin sarrafa wadannan albarkatu, ta yadda za ta kai ga cimma nasarar bunkasa tattalin arzikinta.
Hichilema ya kuma jinjinawa kamfanonin Sin, bisa yadda suke inganta darajar albarkatun dake kasarsa ta hanyoyin zuba jari, kana ya godewa Sin bisa yadda ta bude kasuwanninta ga Zambia da ma sauran sassan nahiyar Afirka baki daya. (Saminu Alhassan)