Wasu Dalibai biyu na Jami’ar Jihar Nasarawa, Keffi (NSUK) sun rasa rayukansu a lokacin da suke ƙoƙarin karbar kayan abinci da gwamnatin Jihar ta ba su a matsayin tallafi don rage radadin tsadar rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki a Nijeriya.
Daliban da ba a bayyana sunayensu ba, sun rasu a safiyar yau Juma’a yayin karbar kayan abincin tallafin.
- An Kama Mutum 10 Bisa Zargin Safarar Mutane A Jihar Nasarawa
- Rundunar ‘Yansandan Jihar Nasarawa Ta Kama Kungiyar Da Ta Sace Kananan Yara 45
Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa daliban da abin ya shafa mata ne, ko da yake majiyar ta ce wasu da dama sun samu raunuka daban-daban a yayin da abun ya faru a wurin taron rabon kayan abincin.
Shugaban kungiyar daliban jihar Nasarawa, Yunusa Yusuf Baduku, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitocin da ke kusa domin kula da lafiyarsu.
Sai dai Baduku bai iya tabbatar da adadin wadanda suka mutu ba nan take.
“Hakika abin da ya faru da safiyar yau a Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi, lamarin abun tausayi ne.
“Bayan shirin da muka yi na rabon kayan abinci ga daliban da za a yi a Jami’ar, kwatsam sai ga su (daliban) sun isa wurin da yawansu, suka kuma yi nasara kan jami’an tsaro da ke wurin.
“Sun kutsa kai cikin wurin da ake rabon, abin bakin ciki shi ne yawancin dalibanmu mata sun samu raunuka da dama, yayin da wasu kuma suka shanye saboda yawan jama’a da ke wurin rabo kayan tallafin.
“A yanzu haka ina cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke garin Keffi, inda muka kawo wasu dalibanmu domin ba su kulawar gaggawa, bazan iya tabbatar da alkaluman wadanda suka jikkata ba a halin yanzu, saboda wasunsu suna asibitin makarantar yayin da wasu kuma suna asibitin makarantar, wasu suna nan a FMC, Keffi suna karbar magani,” a acewarsa.
LEADERSHIP ta rawaito cewa Gwamna Abdullahi Sule ya kara raba kayan tallafi ga daliban manyan makarantun jihar.
Gwamnatin jihar ta fara rabon shinkafa mai nauyin kilogiram 7:5 ga dalibai da ke Lafia babban birnin jihar a ranar Talata.
An rawaito cewa, an kuma ba kowane dalibi kudi naira 5,000 wanda ya kai naira miliyan 35 tare da kayan abinci.
Daliban da suka amfana da rabon sun fito ne daga Jami’ar Tarayya ta Lafia, Isa Mustapha Agwai Polytechnic Lafia, Kwalejin Aikin Gona Kimiyya da Fasaha ta Lafiya da kuma Makarantar koyon aikin jinya da ungozoma ta Lafia.
Gwamna Sule ya yi alkawarin za a mika irin wannan tallafin ga wasu cibiyoyin da ke wajen babban birnin jihar.