Dr. Sani Abdullahi Shinkafi, ɗan jam’iyyar APC kuma tsohon ɗan takarar gwamna a Zamfara, ya tsira da ransa daga hari a Abuja ranar Juma’a, 15 ga Agusta, 2025. Harin ya faru ne jim kaɗan bayan Sallar Juma’a, yayin da yake kan hanyarsa ta komawa gida.
Shinkafi ya bayyana cewa wasu mutane da suka rufe fuska ne sanye da baƙaƙen kaya da muggan makamai ne suka tare motarsa suka kai masa farmaki kafin su tsere a cikin wata motar Prado maras lamba. Ya danganta harin da matsayin sa na ƙwazo da kishin ƙasa wajen magance matsalolin tsaro musamman a Zamfara.
- Ba Sulhu Ko Sassauci Ga Ƴan Bindiga A Zamfara – Gwamna Lawal Dare
- Manoma Sun Caccaki Tinubu Kan Ƙarfafa Shigo Da Shinkafa Da Masara Daga Ƙasashen Waje
Tsohon ɗan takarar gwamnan ya ce ya an sha kiransa ana masa barazana da wasu lambobi da bai san su ba a makon da ya gabata, wanda ya yi imani suna da alaƙa da harin. Ya roƙi shugaban ƴansanda da Daraktan DSS da su binciki lamarin cikin gaggawa, su gano masu hannu a ciki da masu ɗaukar nauyin maharan.
Shinkafi ya jaddada cewa harin ya saɓawa haƙƙinsa na ɗan Adam da kundin tsarin mulki ya tanada, musamman haƙƙin rayuwa da ƴancin faɗin albarkacin baki. Ya kuma bayyana cewa matsayinsa na mai adawa da garkuwa da mutane da aikata laifuka a Zamfara na iya zama dalilin ga wasu masu laifi da shugabannin ƴan fashi na kai masa hari.
Har yanzu hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp