• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ɗan TikTok Tsulange Ya Shiga Hannu Bisa Wanka Da Rigar Mama A Titi

by Abubakar Sulaiman
4 months ago
TikTok

Wata kotun majistare da ke Nomansland a Jihar Kano ta bayar da umarnin tsare wani matashi mai suna Umar Hisham Fagge, wanda aka fi sani da Tsulange a TikTok, bisa zargin aikata alfasha da saɓa wa ɗabi’un al’umma da kuma ƙa’idojin addini.

Mai shari’a Hadiza Muhammad Hassan ce ta bayar da umarnin a tsare shi a gidan gyaran hali har zuwa ranar 3 ga Yuli, 2025, domin ci gaba da bincike.

Tsulange ya gurfana a gaban kotu ne bayan hukumar tantance fina-finai ta jihar Kano ta kama shi bisa bidiyon barkwanci da ya ɗauka yana wanka a titi sanye da tufafin ciki na mata. Hukumar ta bayyana cewa wannan bidiyo ya saɓa wa tarbiyya da al’adun Musulunci da ake mutuntawa a jihar.

  • NDLEA Ta Kai Samame Fitattun Wuraren Shaye-shaye, Ta Cafke Mutane 19 A Kano
  • Wani Matashi Ya Ƙone Kansa A Kano Saboda Yana Son Zuwa Aljanna 

A cewar mai magana da yawun hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, hukumar ta ce bidiyon ya wuce gona da iri wajen cin mutuncin jama’a, kuma yana daga cikin alamomin taɓarɓarewar tarbiyya da ke yawaita a tsakanin masu amfani da kafafen sada zumunta.

Rahotanni sun nuna cewa Tsulange ya saba ɗaukar irin waɗannan bidiyo a manyan tituna, har yana hana ababen hawa wucewa. Rundunar Ƴansandan Kano ta taɓa yin gargaɗi ga masu ƙirƙirar bidiyon abin dariya da su daina toshe tituna don ɗaukar bidiyo.

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025: Benjamin Okezie Kalu

Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya

Hukumar tantance fina-finai ta jihar, ƙarƙashin jagorancin Abba El-Mustapha, ta ce za ta ci gaba da sa ido tare da ɗaukar matakin shari’a kan duk wani da ya yi amfani da sunan barkwanci don yada abin da ya kira da “nishadi mai tada zaune tsaye.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Manyan Labarai

Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025: Benjamin Okezie Kalu

October 26, 2025
Labarai

Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Manyan Labarai

Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus

October 25, 2025
Next Post
Ambaliyar Ruwan Mokwa: Masana Sun Shawarci Gwamnati Kan Matakin Kariya A Nan Gaba

Ambaliyar Ruwan Mokwa: Masana Sun Shawarci Gwamnati Kan Matakin Kariya A Nan Gaba

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025: Benjamin Okezie Kalu

October 26, 2025
An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025

Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025
Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI

Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI

October 25, 2025
An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

October 25, 2025

Daɓid Adeyemi

October 25, 2025
Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.