Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya karɓi sababbin mambobi zuwa jam’iyyar APC, ciki har da Mahbub Nuhu Wali, ɗan uwan Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da wasu manyan jiga-jigan malaman Kwankwasiyya da NNPP.
Cikin waɗanda suka sauya sheƙa akwai Malam Yahaya Abdulkadir Aliyu, Sakataren Kwankwasiyya Ulama Forum, da sauran mambobi 23 na ƙungiyar.
- Binciken Jin Ra’ayin Jama’a Da CGTN Ta Gudanar Ya Shaida Gamsuwar Al’ummun Duniya Da Salon Diflomasiyyar Sin
- ‘Yansanda Sun Kama Mutum 245 Da Miyagun Kwayoyi Da Makamai A Abuja
Sun gana da Sanata Barau a Majalisar Ƙasa, inda suka ajiye jar hularsu domin nuna komawarsu zuwa APC.
Bayan taron, sababbin mambobin APC sun raka Sanata Barau zuwa A-Class Event Centre, inda suka halarci wani taron karɓar wasu ƙungiyoyin magoya bayan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, daga jihohi 19 na Arewacin Nijeriya.
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ne ya jagoranci taron.
Haka nan, wasu manyan jiga-jigan NNPP daga ƙaramar hukumar Gwale, Mahmoud Salisu Gwale da Farouk Ahmed Gwale, su ma sun koma APC.
Sanata Barau ya tabbatarwa da al’ummar Nijeriya cewa kofa a buɗe take ga kowa.
“A matsayina na Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, ina yi wa kowa hidima. Ko da kai ɗan PDP ne, LP, Kwankwasiyya, ko wata jam’iyya, ina tare da kai. Idan kana son shigowa APC, jam’iyyar jama’a, muna maraba da kai. Ƙara yawa, ƙara daɗi!” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp