An samu rahoton mutuwar ɗan wasan gaban ƙungiyar Liverpool, Diogo Jota, sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi a ƙasar Spain.
Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai na ƙasar sun bayyana cewa Jota, ɗan asalin ƙasar Portugal mai shekaru 28, ya mutu ne kusa da garin Zamora da ke Arewa Maso Yammacin ƙasar da safiyar ranar Alhamis.
- Mun Shirya Fuskantar APC Domin Ceto Talakawa – Abubakar Malami
- Buhari Ba Shi Da Lafiya, Amma Yana Samun Sauƙi A Birtaniya — Garba Shehu
Kamfanin dillancin labarai na Spain, EFE, ya ce hatsarin ya auku ne a babban titin Rías Bajas (A-52), kusa da garin Palacios de Sanabria.
El Mundo ya ƙara da cewa ƙanin Jota, mai suna André Jota mai shekaru 26, shi ma ya mutu a hatsarin.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:40 na dare a agogon ƙasar, inda motarsu ta fita daga hanya ta kama da wuta a lokacin da suke kan hanyarsu zuwa Benavente.
Hatsarin ya auku ne kwanaki 10 bayan Jota ya yi bikin aurensa, inda ya wallafa hotunan bikin a shafukan sada zumunta.
Jota ya koma Liverpool daga kulob ɗin Wolverhampton Wanderers a watan Satumban shekarar 2020, inda ya koma kan kuɗi sama da fam miliyan 40.
Tun daga lokacin ya zama babban ɗan wasa a ƙungiyar saboda bajintarsa wajen zura ƙwallo a raga.
Tuni Liverpool da kuma hukumomin Portugal suka fitar da sanarwa kan rasuwar ɗan wasan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp