Wani Sufeto Dansandan da ke aiki a Jihar Kuros Ribas, ya harbe matar abokin aikinsa har lahira tare da jikkata wasu mutane biyu a harbe-harben da ya yi a ranar Lahadi.
Mai magana da yawun rundunar, SP Irene Ugbo, ta tabbatar da faruwar lamarin ga Labarai a birnin Kalaba, inda ta bayyana cewa jami’an Dansandan ya nuna halayyar da ba ta dace ba kafin ya fara harbe-harben.
- Ba Na Goyon Bayan Dakatar Da Gwamnan Jihar Ribas – Ndume
- Bututun Iskar Gas Ya Sake Fashewa A Ribas
Ugbo, ta ƙara da cewa jami’in, naaiki ne a Cibiyar ‘Yansanda ta Atakpa, ya dawo daga aikin dare a wani bankin ‘Microfinance’ kafin afkuwar lamarin. Ta kuma bayyana cewa tuni an kama wanda ake zargi, inda su kuma waɗanda suka jikkata ke samun kulawar likitoci a asibiti.
Bincike ya nuna cewa ɗansandan ya fara nuna alamun taɓun hankali tun bayan dawowarsa daga aikin dare, inda ya rufe ƙofar shiga ofishin ‘yansandan tare da hana kowa fita ko shigowa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp