Mataimakin kwamishinan ‘yansandan Nijeriya, Daniel Amah, wanda ya shahara da ƙin karɓar cin hancin dala 200,000, ya musulunta a wani biki da aka gudanar a fadar Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II.
A yayin taron wanda ya gudana a ranar Talata 7 ga watan Janairun 2025, Amah ya karɓi addinin Muslunci tare da zaɓar Muhammad a matsayin sabon suna, inda Sarkin Kano ya buƙace shi da ya nemi ilimin addinin Musulunci da kuma rike ƙaidojin addini kana ya yi masa addu’ar Allah ya sanya shi cikin salihan bayinsa.
Ya kuma gargade shi da ya riqi kyawawan ɗabi’unsa, tare da ci gaba da girmama iyayensa da biyayya garesu ba tare da la’akari da bambancin addininsu ba.
Idan za a iya tunawa Amah, a baya ya samu karramawa lokacin da yake shugabantar ofishin ‘yansanda a ƙaramar hukumar Nasarawa ta jihar Kano, a lokacin da ya ƙi amincewa da cin hancin dala 200,000 daga wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne bayan sun sace sama da dala 750,000 daga hannun wani ɗan canji kuɗaɗen ƙasar waje a watan Afrilun 2022.
Dalilin haka hukumar kula da aikin ‘yansanda ta karrama Amah, tare da ƙara masa matsayi daga babban Sufeton ‘yansanda zuwa mataimakin kwamishinan ‘yansanda, sannan kuma tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya karrama shi da lambar yabo ta 2022 mai daraja ta aikin gwamnati.