Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da amfani da ƙarfi wajen hana ‘yan hamayya ‘yancin faɗin albarkacin baki.
Atiku, ya mayar da martani ne kan kalaman Sakataren Yaɗa Labaran APC, Felix Morka, wanda ya gargaɗi Peter Obi na jam’iyyar LP kan tsokacinsa game da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
- Awannin Da Sallamarsu A Matsayin Kwamishinoni, Gwamnan Bauchi Ya Naɗa 3 A Matsayin Mashawarta
- Ana Kara Zuba Jarin Waje A Kasar Sin A Sabuwar Shekara
Mai magana da yawun Atiku, Abdurrashid Uba Sharada, ya ce gwamnatin APC tana ɗaukar matakan murƙushe ‘yan adawa, wanda hakan barazana ce ga dimokuraɗiyya.
Sai dai APC ta ƙaryata wannan zargi, inda ta ce jam’iyyun adawa na cusa ma’ana ga kalaman da ba su kai ga haka ba.
Bala Muhammad, mai magana da yawun APC, ya ce abin da ake yi wa Nijeriya zai kawo alfanu a nan gaba, kodayake yanzu yana da ciwo.
A halin yanzu, ‘yan Nijeriya na ci gaba da kokawa kan tsadar rayuwa da ta biyo bayan cire tallafin man fetur a shekarar 2023.