Tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma tsohon ministan babban birnin tarayya (FCT), Malam Nasir El-Rufai, ya zargi gwamnatin jihar Kaduna da ɗaukar nauyin ƴan daban da suka tarwatsa taron jam’iyyar adawa ta ADC a ranar Asabar.
A wata hira da aka yi da shi a shirin Sunday Politics na gidan talabijin ta Channels da wakilinmu ya kalla, El-Rufai ya yi watsi da iƙirarin rundunar ƴansandan Kaduna cewa jam’iyyarsu ce ta gayyato ƴan daba.
- ADC Ta Bukaci Tinubu Ya Kafa Dokar Ta Baci A Katsina Da Zamfara Kan Rashin Tsaro
- Hatsarin Jirgi: Babu Batun Zagon-ƙasa Ga Harkokin Sufurin Jiragen Ƙasan Abuja-Kaduna – Gwamnati
Ya bayyana wannan magana a matsayin “shashanci” tare da jaddada cewa ƴansandan da kansu sun bayar da kariya ga ƴan ta’addan da suka yi ɓarna a wajen. “Wauta ce a ce ni zan gayyato ƴan daba domin su farmaki taron jam’iyyata. Ƴansandan suna wurin, suna sane da abin da ya faru. Sun ba wa ƴan dabbar kariya. Waɗannan ƴan dabar gwamnati ce ta ɗauki nauyinsu,” in ji shi.
El-Rufai ya ƙara bayyana cewa tun a farkon shekarar nan ya rubuta ƙorafi ga Sufeton Ƴansandan Nijeriya kan wasu jami’an ƴansanda a Kaduna da ake amfani da su wajen tsoratar da ’yan adawa tare da yin garkuwa da su. Ya ce har yanzu yana jiran sakamakon binciken da aka fara a kan lamarin.
Tsohon gwamnan ya nuna takaici kan yadda tsarin aikin ƴansandan a Nijeriya ya taɓarɓare. A cewarsa, maimakon jami’an tsaro su kare al’umma, yanzu ana amfani da su wajen ba da kariya ga masu haddasa tashin hankali. “Wannan iƙirarin na ƴansandan cewa ADC za ta gayyato ’yan daba domin su tarwatsa taronta alama ce ta durƙushewar tsarin ƴansandan. Da muna da ƴansanda, yanzu kuwa inuwa ce kawai ta yi saura,” in ji shi.
Ya kuma tuna da tsohon abokin ajinsu wanda ya kasance tsohon Sufeton ƴansanda, marigayi Solomon Arase, wanda ya rasu a ranar Lahadi a Abuja bayan gajeriyar rashin lafiya. El-Rufai ya bayyana shi a matsayin mutum nagari, yana mai cewa tsarin ƴansanda na yanzu ya sha bamban da lokacin da Arase ya jagoranta. Daga ƙarshe, ya ce zai sake rubuta ƙorafi ga IGP da kuma hukumar kula da ƴansanda (PSC), yana mai gargadi cewa idan jami’an tsaro suka zama kariya ga masu tada fitina, to hakan zai kai ƙasa ga rugujewa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp