Rundunar ƴansanda a jihar Katsina sun saka kyautar naira miliyan 50 ga duk wanda ya taimaka ya bayar da bayanai da za su taimaka wajen kama ƙasurguman ƴan bindiga biyu da suka addabi wani yanki a jihar Katsina.
Ana zargin ƴan bindigar su ne, Modi Modi da takwaransa Jan Kare da kai muggan hare-hare a ƙananan hukumomin Safana da Ƙanƙara a baya-bayan nan.
- Gwamnati Katsina Ta Kashe Miliyan 50 Wajen Gyara Motocin ‘Yansanda 15
- ‘Yan bindiga Sun Kashe Mutum 6 A Jihar Katsina
Wannan dai na cikin wata sanarwa da kakakin ƴansandan Jihar Katsina Abubakar Sadiq ya fitar.
Sadiq ya ce rundunar za ta tabbatar da ta ɓoye sunayen duk wanda ya taimaka ya ba da wani bayani da zai taimaka wajen kama waɗannan mutanen biyu.
Ya kara da cewa wannan na cikin matakan da ƴansanda da sauran takwarorinsu ke dauka wajen ganin an dawo da zaman lafiya a jihar.
Sanarwar ta ce “Rundunar ƴansandan jihar Katsina ta sanya naira miliyan 50 ga duk wanda ya taimaka wajen bayar da bayanan da za su taimaka wajen kama Modi Modi da Jan Kare da ke addabar yankin ƙananan hukumomin Safana da Ƙanƙara a jihar Katsina”.
Kakakin ƴansandan ya yi kira tare da ƙarfafa wa mutane guiwa da su fito su ba da bayanan da za su taimaka wajen kawar da ƴan bindigar.
Ya ce ga duk mai wani bayani da zai taimaka za su iya tuntuɓar waɗannan lambobin kamar haka: 07015142112, 08023871144.