‘Yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da takwaransa na Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, a ranar Lahadi, 12 ga watan Yuni, 2022, jam’iyyar LP ta Peter Obi, da wasu fitattun ‘yan Najeriya da masu fafutukar tabbatar da dimokuradiyya za su ajiye furanni don tunawa da wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka soke ranar 12 ga watan Yunin 1993, marigayi Cif MKO Abiola.
Shugaban kwamitin shirya bikin ranar dimokradiyya na ranar 12 ga watan Yuni, Farfesa Anthony Kola ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.
- Atiku Zai Yi Wa Tinubu Kwab Ɗaya, Don Ba Tsaransa Ba Ne, In Ji PDP
- Ni Zan Zaɓi Mataimakina Da Kaina – Tinubu
Ya ce, “A taron tunawa da zagayowar ranar dimokaradiyya na ranar 12 ga watan Yuni, wadda fitattun ‘yan uwa masu rajin kare dimokradiyya a Nijeriya suka kira, na sanar da cewa, ranar za ta karbi bakuncin fitattun ‘yan Nijeriya da masu fafutukar tabbatar da dimokuradiyya.
A ranar Lahadi, 12 ga watan Yuni, 2022, a gidan MKO Abiola, wanda ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 12 ga watan Yuni, 1993, wanda ya rasu a gidan yari saboda ya ki yin watsi da wa’adin tarihi da ‘yan Nijeriya suka ba shi kyauta.
“Wannan taron mai cike da tarihi wanda za a gudanar a harabar gidan MKO Abiola da ke Legas mai suna Cibiyar Dimokuradiyya ta Nijeriya ta kungiyar 12 ga watan Yuni, an yi shi ne da nufin tabbatar da amincewa da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar dimokuradiyyar Nijeriya a hukumance.
“Don haka, ana sa ran taron mai cike da tarihi za a gudanar da addu’o’i da karramawa wasu da tunawa da ‘yan mazan jiya jarumai da jarumta a fannin dimokuradiyyar Nijeriya da kuma shimfida furen karramawa kan kabarin MKO Abiola domin tunawa da shi, da irin sadaukar da rayuwarsa mai daraja wajen kare hakkinsa.
Damar da al’umar Nijeriya suka ba shi a ranar 12 ga watan Yunin 1993 a lokacin haifuwar mulkin dimokaradiyya a Nijeriya.
“Wasu daga cikin jiga-jigan ‘yan Najeriya da aka gayyata don yin jawabai da karramawa a wajen taron mai taken ‘Fatan Zaben 93 da Yuni 12: Darasi don gudanar da sahihin Zabe a 2023’ su ne Farfesa Wole Soyinka, shugaban taron; Sanata Bola Ahmed Tinubu, da Waziri Atiku Abubakar da Peter Obi, Cif Ayo Adebanjo, Janar Alani Akinrinade, Farfesa Pat Utomi, Dr Olisa Agbakoba, Mr Femi Falana, Mr Mike Ozekhome, Dr Oby Ezekwesili, Sanata Shehu Sanni, Cif Dele Momodu da dai sauransu.
“Hakazalika, an yi gayyaci dukkan gwamnoni masu goyon bayan 12 ga watan Yuni da masu ruwa da tsaki domin su yi jawabi tare da nuna godiya a wajen taron tare da gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu a matsayin babban mai masaukin baki.”