Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC), ta tabbatar da mutuwar mutane 15 tare da jikkata wasu biyar a wani hatsarin mota da ya afku a Jihar Kogi.
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN), ya ruwaito cewa hatsarin ya faru ne tsakanin J-5 Boxer bas da wata tankar mai, a Koton-Karfe kan babbar hanyar Lokoja zuwa Abuja da misalin karfe 7:30 na safiyar ranar Talata.
- Ana Sa Ran Birtaniya Za Ta Fice Daga Tsibiran Malvinas Bayan Daidaita Ikon Mallakar Tsibiran Chagos
- Man U Na Shirin Yin Wuf Da Giroud Don Maye Gurbin Ronaldo
Kwamandan FRSC a Kogi Stephen Dawulung, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an garzaya da mutanen biyar da suka jikkata zuwa asibitin Ideal da ke Koton-Karfe domin ba su kulawar gaggawa.
Dawulung, ya ce an ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiye gawa na babban asibitin tarayya (FMC) da ke Lokoja.
Kwamandan sashen, ya bayyana cewa musabbabin hatsarin ya faru ne saboda keta dokokin hanya da direban motar bas din ya yi, wanda ya ke tukin mota a lokacin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Lokoja.
“Direban bas din ya bar hannunsa yayin da yake tuki sai ya yi karo da wata motar dakon mai da ke zuwa.
“Alhamdulillahi motar dakon man fetur din ba ta tashi ba, da lamarin ya zama abun tashin hankali da damuwa.
“Abin takaicin shi ne, motar bas din tana dauke da tarkacen karfe da fasinjoji 17, 15 daga cikinsu an murkushe su kuma sun mutu a yayin da suka yi karo da juna.
“Abin takaici ne yadda ake cin zarafi da yawa da yadda ake karya dokar zirga-zirgar ababen hawa.
“Motocin da aka kebe don daukar kayayyaki ya kamata su dauki kaya kawai ba fasinjoji ba kamar yadda wannan lamari ya faru ” in ji Dawulung.
Sai dai kwamandan FRSC, ya jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa, ya kuma shawarci masu ababen hawa da su rika bin ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa domin kaucewa hatsari.