Nasir S Gwangwazo" />

2015: Ba A San Alfarmar Jonathan Ba – Abdulsalam •Tsoron Tuhuma Ke Hana Shugabanni Mika Mulki – Goodluck

Tsohon Shugaban Nijeriya, Janar Abdulsalam Abubakar, ya bayyana cewa, har yanzu ’yan Nijeriya ba su san irin alfarmar da tsohon shugaban kasar, Dr. Goodluck Ebele Jonathan, ya yi wa kasar ba a yayin zaben 2015 lokacin da ya amince ya amshi kayin zabe har ma ya taya shugaban kasa na yanzu, Muhammadu Buhari, murna lashe zaben.

Bugu da kari, Dr. Jonathan ya bayyana cewa, al’adar nan ta tuhuma da bi-ta-da-kulli ga tsofaffin shugabanni a Afrika na daga cikin dalilan da su ka sanya su ke tsohon mika mulki ga magadansu ko ’yan adawarsu.

Tsofaffin shugabannin su na magana ne a taron kasashen duniya kan zangon mulki da a ka gudanar a Niamey, babban birnin kasar Nijer, a maon jiya.

Tsohon Shugaban mulkin sojan, Janar Abdulsalam, ya kara da cewa, Dr. Goodluck Jonathan, wanda ya mika wuya cikin sauki bisa kayin da ya sha a 2015, duk da kasancewarsa shugaba mai ci a lokacin, har yanzu bai samu yabon da ya cancance shi daga ’yan Najeriya ba bisa wannan abinda ya yi na tserar da kasar daga fada wa tashin hankali.

Idan za a iya tunawa, a na tsaka da tattara sakamakon zaben 2015 ne, tsohon Shugaba Jonathan ya kafa tarihin rawar gani, inda ya buga wa Shugaba Buhari waya ya na mai taya shi murnar lashe zaben, duk da cewa, ba a sanar da hakan ba a hukumance bayan da ya lura da cewa, zai yi wahala ya kai ga nasarar lashe zaben bisa la’akari da yadda sakamakon ke fitowa.

A karshen sakamakon kuwa, Buhari ya samu kuri’u 15,426,921, inda ya kayar da Jonathan, wanda ya samu kuri’u 11,153,118.

Wannan shi ne karon farko da shugaba mai ci ya fadi zabe a tarihin Najeriya ta hanyar zabe kuma ya taya wanda ya kayar da shi murna, inda wayar da ya buga ta kashe hasashen da a ka yi na samun tashin hautsini da rikicin bayan zabe, jim kadan bayan da wakilinsa a hedikwatar tattara sakamakon da ke Abuja, Mr. Godsday Orubebe, ya tayar da kayar baya a wajen, ya na mai zargin shugaban hukumar zabe na lokacin, Farfesa Attahiru Jega, da nuna mu su bambanci.

“Mutane su na yawan yaba wa Kwamitin Zaman Lafiya da na ke jagoranta da cewa mu ne mu ka janyo hankalin Jonathan ya saduda ga Buhari, to amma ba su yaba wa shi Shugaba Jonathan kan matakin da ya dauka, domin shi ne a karan-kansa ya amince da daukar matakin taya Buhari lashe zaben 2015,” in ji Janar Abubakar.

Shugaban Kwamitin Zaman Lafiyar na Nijeriya, wanda ya hada da tsofaffin shugabannin kasar, masu-fada-a-ji da malamai da sarakuna, ya kara da cewa, “duk da ya ke bayan fara sanar da sakamakon mun yi magana da dukkan ’yan takarar shugaban kasar, amma ba mu zauna gaba da gaba da Jonathan mun saka shi ya aikata hakan ba. Shi ne ya yi a kashin kansa.”

Daga nan sai Janar Abdulsalam, wanda shi ne tsohon shugaban mulkin soja na karshe a Nijeriya da ya mika mulki ga farar hula har yanzu su ke mulki tun daga 1999, ya ce, Jonathan ya cancanci a yaba ma sa matuka gaya bisa fargabar da ya cire wa ’yan Nijeriya da karfin gwiwar da ya bai wa kasashen duniya kan Nijeriya da cewa, dimukradiyyar kasar yanzu ta nuna, saura romo kawai.

A nasa jawabin, Goodluck Jonathan, wanda ya yi magana kan dalilan da su ke janyo neman tazarce a kasashen Afrika ta karfi da yaji, ya ce, sai magadansu sun rika kawar mu su da kai, kafin a kai ga samun saukin hakan.

A ta bakinsa, “mu samar da yanayin da zai sa tsofaffin shugabanni su ji a ransu cewa, akwai wata kyakkyawar rayuwar bayan sun bar mulki. Yanayin yadda mu ke tafiyar da kanmu a matsayin shugabanni masu mulki da masu barin gado ya na da muhimmanci. Matakin farko shi ne mu rage wa shugabanni masu barin gado fargabar barin ofis.”

Daga nan sai Jonathan ya yi tir da dabi’ar nan ta mayar da masu mulki tamkar alloli, ya na mai cewa, “wasu lokutan a Afrika mu ne matsalar kanmu da kanmu, domin mu na kallon shugabannin kasa tamkar wasu alloli. Don ka na matsayin shugaban kasa ba ka yi ya Allah ba. Mu na da al’ada ta bambadanci. Mu na iya saka wa shugabanni girman kan da ba su da shi ta hanyar ba su matsayi da kimar da ba su kai ba.

“Mu na yi mu su bambadancin da da har za su fara jin kansu tamkar kananan alloli. Idan su ka fara tunzura shugaba su na nuna ma sa cewa kamar Allah ya ke kuma shi kadai zai iya mulkar kasar, sai ya fara tunanin cewa, babu wanda ya isa ya kawar da ‘allah’.

“Idan ka mayar da Shugaban Kasa tamkar Allah, kada ka yi tunani zai yarda ya bar mulki. Dole ne kafafen yada labarai da kungiyoyin farar hula su cigaba da nunar da shugabannnin kasa fahimtar cewa samuwarsu na da matukar muhimmanci, amma kasancewarka shugaban kasa ba ya nufin ka fi kowa ba ne. ’Yan kasa ke haifar da samuwar kananan alloli har su dauka cewa, ai wannan allan bai sauka daga mulki.”

Abdulsalam da Jonathan dai na daga cikin wadanda su ka gabatar da kasidu a taron, wanda cibiyar raya dimukradiyya ta National Democratic Institute (NDI) ta shirya a Yamai.

Exit mobile version