Kwamared Ruwan Godiyar Da Na Sani? — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MUKALA

Kwamared Ruwan Godiyar Da Na Sani?

Published

on


Muhammad Bashir Usman Ruwan Godiya, wannan shi ne cikakken sunansa na yanka, amma jama’a da dama suna kiransa da Ruwan Godiya saboda dan garin ne kuma yana amfani da suna garin a matsayin lakabi.

Garin Ruwan Godiya da ke cikin karamar Hukumar Faskari a jihar Katsina nan ne mahaifarsa, wani abin burgewa shi ne, bai taba boyewa ba ko kunyar fadin cewa an haifeshi a kauye ba, yana alfahari da wannan gari na su, kuma ya bada taimako ga mutanen wannan gari, kai shi ne ya yi silar fice da sunnan wannan gari na Ruwan Godiya.

Wannan suna na Ruwan Godiya babu wanda bai san shi a cikin garin Katsina, kuma an san shi ta fannoni daban-daban, wasu sun shi a matsayin malamin makaranta wasu kuma sun san shi a gidan rediyo wasu kuma sun shi ne a fannin gwagwarmaryar kungiyoyin sa ido.

Ko ma dai ya ya, ni nasan kwamared Bashir Usman Ruwan Godiya a matsayin malamina kuma na san shi tun tuni saboda haka zan yi magana ne akan yadda na san shi, sannan in alakanta sanayar da sabon mukamin da Gwamna Aminu Bello Masari ya nada shi a matsayin mai  baiwa gwamna shawara akan ilimi mai zurfi.

Tun daga lokacin da na san shi har zuwa yau din nan ban ga ya canza daga yadda na san shi,  duk da ikirarin da wasu ke yi cewa yanzu ya canza, duk da kasancewarsa mai shige da fice da kuma sa ido akan al’amuran da ke zuwa suna dawowa.

Kasancewata dalibinsa na tsangayar karatun aikin Jarida a kwalejin kimiya da fasaha ta Hassan Usman Katsina ya taka mahimmiyar rawa wajan ganin na samu nasara a karatuna da na yi, haka kuma duk wani dalibi da ya yi karatu a wannan fanni ya san da zaman Ruwan godiya wanda ake yi wa kirari da kaifi daya, ya san mahimmacinsa a wannan bangare yasan irin gudunmawar da yake badawa ga dalibai da kuma aikin jarida a jihar Katsina baki daya.

Duk malamin da ke bangaran tsangayar koyan aikin jarida da ke Hassan Usman Katsina sun san abinda suke yi, kuma har gobe wannan yasa ake ganin martabar wannan fanni a duk fadin wannan kwaleji, Malaman sun fita daban da sauran Malamai sun waye fiye da tunanin mai tunani suna da ilimin addini bakin gwargwado sannan sun yi zarra a zamanance.

To shi Kwamared Ruwan Godiyar da na sani, ya sha banban da sauran Malamai domin kuwa ya tserewa tsara, shi ne kadai Malamin da jinina ya fi haduwa da shi tun da na san shi, kai shi ka dai Malamin da idan dalibi ya kasa gane koyawarsa to sai dai mutun ya hakura da karatu zai fi yi masa sauki.

Allah Ya hore masa iyawa, ya zama gwani na gwanaye a tsakanin Malaman tsangayar koyan aikin jarida ta Hassan Usman Katsina, ya san mutunci mutane baya raina kowa, zai yi ma’amula da kai gwargwadon yadda ya fahimceka, zai baka hakkinka idan ya biyo ta hannunsa, tunda muka san shi ba mu taba jin wani abin assh game da shi ba, amma mun ji a wasu malamai.

Shi ne kadai zai gaya maka yadda ya yi rayuwarsa ta kauye kafin ya shiga birni, amma wasu ko sunan unguwarsu ka fada, sai su ce ka maida su ‘yan kauye, shi ne kadai idan yana koyarwa ba a kosawa ko gajiya, shi ne kadai dalibai suka fi san koyarwasa fiye da ta kowa.

Gaskiyar magana yana sona, kuma har gobe da shi nake tutiya da kuma inkiya idan anan bukatar takarduna a wani wuri, nine kadai dalibin da yake wasa da shi fiye da kowa, wannan ya sa nake son haduwa ko yin aikin ko taro tare da shi, na fi san shi fiye da sauran malamai saboda yadda jinina ya hadu da shi, amma suma sauran ba kashin yadawa bane. (an gaisheku sauran Malamai)

Kamar yadda na ce, wasu sun san shi, a gidan rediyo wannan  haka yake, yana daga cikin mutanen da Allah ya yi wa nasibi da fadar gaskiya wanda ta zama abu mai wahala a wannan lokaci, kar ka yi tunanin cewa kuna tare ko ya sanka ko yana rage maka wuri, idan fadan gaskiya ya zo akanka to a cikin rediyo zaka ji shi ya daboma ita ba gyara.

Wannan ya sa ya yi fice ya kuma kara yin suna a gidanjen al’umma, duk macen da ke sauraran rediyo a cikin garin Katsina ta sa Malam Bashir Usman Ruwan Godiya kuma suna san jin ana hira da shi akan kowace irin matsala, domin suna yarda da abinda yake fada.

Yana da kwarjini,  yana dalibai da daman gaske a mafi yawan kafefen yada labarai wannan yasa yake da karfin fada aji, yasan manya a siyance duk da cewa shi ban dan siyasa ba ne, yana ma’aumla da kungiyoyi daban-daban kasancewa shugaban gamayyar kungiyoyin sa ido, ya iya magana ga kuma iya barkwanci wanda dole ya sa ka dariya, ance wannan yana daya daga cikin sirrin nasarar iya koyawarsa a cikin aji. Baya zalunci kuma baya goyan bayan a yi zalunci.

Ya yi tafiye-tafiya a cikin kasa da kuma kasashen waje domin gabatar da mukaloli a fanni daban-daban, anan cikin gida ma har gobe idan za a yi wani muhimmin aiki da ya shafi aikin jarida to su Ruwan godiya ne kanwa uwar gami, yana ciki tsun dum.

A bisa wadannan ‘ya kadan daga cikin halayarsa da na ambata wandada suka san shi sani na hakika za su tabbatar da cewa kwamared bai canza kuma ni da su muna da tabbacin ba zai canza daga yadda muka san shi ba. Sai dai wani iko na ubangiji.

Kwananan kamar daga sama sai jin sanarwa muka yi cewa gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya ba shi mukamin mai baiwa gwamna shawara akan ilimi mai zurfi wato ya zama daya daga cikin ‘yan majalisar zartarwa a jihar katsina

Wannan sanarwa ta zo da tambayoyi da daman gaske musamman ga wadanda suka san Muhammad Bashir Usman Ruwan Godiya, wasu na ganin kamar gwamna Masari ya dauki kaya da kansa ya saka cikin gwamnatinsa domin yana da wahala a iya daidaitawa da dan gwagwarmaya a harkar gwamnati wanda take da rudani musamman idan an zo yi rashin gaskiya.

Ni kima na ce idan dai Ruwan Godiyar da sani na ne, ba abinda zai faru sai alheri  sai ma kara daidaita al’amura domin kuwa shi aikin gwamnati a fili yake, da zaran ka gane iya huruminka sai ka tsaya nan wanda kuma Ruwan godiya ya kware wajan kaucewa abinda ba ruwansa.

Wasu na ganin tunda gwamnati ta jefa shi cikinta an rufe bakin tsanya, saboda ko ba komi yanzu yana cikin dumu-dumu saboda haka bakin da ya ci zai ji kunya yin magana, wannan tunanin wasu da ko dai ba su san ruwan godiya ba ko kuma suna yi masa kallon nesa.

Ni kuma cewa na yi, in dai Ruwan Godiyar da sani ne, haka ba zata ta taba faruwa ba, ina son jama’a su rubuta su ajiye, Ruwan godiya zai zama abin bada misali a matsayin da aka ba shi, zai yi iyakar kokarinsa wajan ganin ya sauke nauyin da ya hau kansa, zai yi kokarin ba marada kunya ta hanyar tsayawa akan gaskiya wanda kowa ya san shi  da ita.

Akwai masu tunanin Ruwan Godiya ya matsawa gwamnatin da fadin gaskiya kuma an rasa yadda za a yi da shi, shi ne aka tsunduma shi cikin gwamnati domin dai a huta da matsalarsa har suna bada misali da yadda tsohon gwamna Edo Kwamared Adams Oshomhole ya addabi gwamnatin tarayya a wancan lokacin  amma ana cewa shi ya ci zabe, sai ya koma kamar anyi ruwa an dauke. (shiru kaki ji Malam ya ci shirwa)

Ni kuwa kullun cewa nake indai Ruwan Godiyar da sani ne, su sa ido su yi kallo duk ranar da aka zo mashi da wani batu na rashin gaskiya to daga wannan rana jama’a za su kara gane wanene Muhammad Bashir Usman Ruwan Godiya acikin gwamnati, wannan rana za a gane yanzu akwai ‘yan kara tsaye, wato mai fadin gaskiya komin da-cin-ta sannan ko da kuwa wani abu zai faru.

Akwai sauran maganganu da tambayoyi game da wannan mukami da aka baiwa kwamared Muhammad Usman Ruwan Godiya wanda zan yi bayaninsu a rubutu na gaba da wasu tunane-tunane da jama’a ke yi game da wasu matsaloli da ake hange tare da kwamared Ruwan Godiya. Ni kuma na dage da cewa in dai Ruwan Godiyar da na sani ne…?

 

Advertisement
Click to comment

labarai