Connect with us

WASANNI

Arsenal Da Liverpool Su Na Zawarcin Ivan Rakitic

Published

on

Rahotanni daga kasar sipaniya sun bayyana cewa kungiyoyin Arsenal da Liverpool suna zawarcin dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Ivan Rakiic dan kasar Croatia bayan da dan wasan yaki kara kwantaragi.

Rakitic, wanda yakoma kungiyar kwallon kafa ta Barcelona daga kungiyar Sevilla a shekarar 2014 yana ganin kamar komawar dan wasa De Jong kungiyar zai sa ya daina samun wasanni da yawa yasa yafara tunanin barin kungiyar tun kafin lokaci ya kure masa.

De Jong  yakoma Barcelona ne daga kungiyar kwallon kafa ta Ajax Amsterdam akan kudi fam miliyan 60 wanda hakan yasa dan wasan yafi kowanne matashin dan wasa tsada a kungiyar tun daga lokacin da aka kafa ta.

Ita ma kungiyar kwallon kafa ta Jubentus tana daya daga cikin kungiyoyin da suke zawarcin dan wasan dan asalin kasar Croatia wanda yabuga wasanni 33 a gasar laliga a wannan kakar yayin da Manchester United ma take ganin zata gwada taya dan wasan.

Sai dai kungiyar kwallon kafan ta Barcelona bata da niyyar siyar da dan wasan kamar yadda rahotanni suka bayyana sakamakon tana bukatar matasan ‘yan wasa a kungiyar saboda tsufan da ‘yan wasan kungiyar suka farayi wato  Sergio Basquet sannan kuma Iniesta yabar kungiyar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!