Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

’Yan Fashi Sun Kashe Mai Gadi Da Jikkata Mutum Biyu A Asaba

Published

on

Wasu gungun ‘yan fashi da makami sun kashe wani mai gadi mai suna Mista Jerry, tare da jikkata mutum biyu a wani gidan mai kusa da rukunin gidajen ‘yan sanda  da ke cikin garin Asaba ta Jihar Delta. Kwamishinan ‘yan sandar jihar, Mista Adeyinka Adeleke, shi ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Talata. Ya ce, “garkiya ne, domin na samu wannan labara tun da sassafe. Mutum da a ka kashe mai gadi ne a gidan mai.Ya yi kokari ya tashi, inda daga baya ya mutu.”

Adeleke ya kara da cewa, ‘yan fashin sun yi awon gaba da sama da naira miliyan daya daga gidan man, yayin da sun kwace naira 200,000 daga hannun mutane, har yanzu ba a samu nasarar cafke wani daga cikin ‘yan fashin ba.

Majiyarmu ta labarta mana cewa, ‘yan fashin sun mamaye gidajen mai na B2 Energy da kuma Berun da  suke kan titin Okwe ranar Litinin, sun dalle kofofin gidajen man, inda su ka yi awon gaba da miliyoyin Nairori.

Wani ma’aikacin gidan mai ya bayyana cewa, “lokacin da mu ka zo aiki da safe, mu samu mai gadin gidan mai, Mista Jerry ya mutum, inda a ka daure shi tare da rufe fuskansa da bikiti a cikin bayi.nan take mu ka sanar wa mutane. “A wannan lokaci, an harbi wasu masu gadi hausawa daga wani gidan mai wanda ya ke makwabtaka da mu, inda su ma a ka daure su, amma ba a rufe musu fuskansu ba.

“’Yan fashin sun balle kofarmu mai karfi, sannan an kuma bayyana mana cewa, sun balle kofar dayan gidan man kafin su shiga gidana man, sun yi amfani da hutun karshan mako, inda su ka kwashe kudin da mu ka sayar da mai.”

An bayyana cewa, masu gadin guda biyu wadanda a ka jikkata na gidan mai Berun, su na asibiti su na jinya, domin ‘yan fashin sun jire musu hakora.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa, ‘yan fashi sun yi fashe a gidajen mai guda biyu ba tare da yin harbi ba, domin kar masu gadin rukunin gidajan ‘yan sanda su ji. “Mun yi mamakin yadda mu ka tashi da safe mu ka tarar an yi fashi a gidajen mai guda  biyu har ma da kashe mai gadi. Ba mu ji wani karar bindiga ba, domin idan da sun yi harbi, to da jami’an tsaro sun ji su,” in ji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: