Connect with us

KIWON LAFIYA

Kungiyar Likitoci Ta Kasa Ta Hukunta Likitoci Biyu

Published

on

Kotun da kungiyar likitoci ta kasa ta kafa ta hukunta likitoci biyu, wadanda ta samu da laifin wasa da aikinsu da kuma nuna halin ko in kula. Likitocin su ne Godwin Maduakor da kuma Nwikwu Bitalis wadanda a ka yanke wa hukuncin.

A hukuncin da aka yanke wandfa shi kuma Shugaban kotun Abba Hassan ya karanta, ya nuna cewar an samu Mista Maduakor, da aikata laifi indann aka yi la’akari da zarge- zargen da ake zargin shi da aikatawa, an dakatar da shi watanni shida, saboda laifi na daya, da kuma wata auku saboda laifi na biyu. Jami’in ya bayyana cewar duka  hukuncin da aka yanke ana iya hada su gaba daya.

Mista Maduakor yana daya daga cikin Likitoci tara daga Asaba wadanda suke fuskanta shari’a, saboda zargin da ake yi masu da wasa da aikin su, da kuma nuna halin ko in kula, wajen lura da wata mata mai Juna Biyu wadda ake kira da suna Rita Uche Ogbuego”.

Sauran wadanda suma suke fuskantar shari’ar daga cibiyar kula da lafiyar al’umma ta Asaba jihar Delta, sun hada da Sunday Abiodun, Oyefara Babatunde, Okoye Pascal Nnamdi, Anunnobi Chijioke Ralu, Adigba Ese Onodjohwoyobwe, Ogwu Robinson Onyeka Chukwu, Okoye Chukwuka da kuma Iyiola Akeem Adewale.

Duk sai suka ki amincewa da cewar sun aikata laifi, bayan da aka karanta masu zargin sun aikata laifi, bayan da aka gama karanta masu daya bayan daya wato ko wanne da nahi.

Hakanan shima Mista Bitalis an kawo shi gaban kotun akan laifi daya da aka zargin shi da aikatawa, na wasa da aikin shi da kuma nuna halin ko in kula, ”saboda ya bude asibitin shi ya kuma tafi wani wauri, ba tare da ya bar wani kwararre ba, saboda ya kula da duba marasa lafiya.”

Wannan halin na shin a barin wurin aikin shi ya yi sanadiyar mutuwar wani mara lafiya, wanda ya zo saboda ya samu damar a duba shi ya samu magani, lokacin da baya nan.

Mista Bitalis dai an dade da dakatar da shi daga aiki, tun shekarar 2016,  ya ki yarda da amsa laifin shi, lokacin da aka fara cigaba da sauraren ita shari’ar cikin watan Afrilu na 2019.

Ita dai kungiyar it ace wadda take daukar matakai na ganin cewar shi aikin na Likita da kuma sauran kwararru da suke karkashin kungiyar suna tafiyar da ikinsu lafiya lau. Bugu da kari kuma duk wani dan kungiyar wanda ya aikata abinda bai dace ba, wanda kuma ya keta dokokin kungiyar ana iya daukar mataki ko kuma matakai akan shi ko kuma su.

Ita dai kotun ta kungiyar ta Liktoci tana da dama ko kuma ikon yin hukunci, kamar dai yadda sauran kotuna suke yi, amma kuma duk wani hukuncin data yanke ana iya kalubalantar shi a kotun daukaka kara.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: