Connect with us

WASANNI

Zakarun Afrika: Pillars Za Ta Kafa Sansani A Kaduna

Published

on

Shugabannin gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars sun bayyana cewa zasu tashi tare da ‘yan wasan kungiyar domin komawa jihar Kaduna inda zasu kafa sansanin da zasu tashi zuwa kasar Ghana buga gasar cin kofin zakarun Africa zagaye na biyu.

Kamar yadda kociyan kungiyar ya bayyana, tuni ‘yan wasan kungiyar sun bar jihar Kano a ranar Lahadi inda zasu cigaba da shirye shiryensu a Kaduna yayinda daga nan ne kuma zasu tashi zuwa kasar Ghana a sati mai zuwa.

Tawagar zata shafe kwanaki uku a jihar Kaduna daga nan kuma zasu sake tsallakawa zuwa babban birnin tarayya Abuja domin hawa jirgin da zai kaisu babban birnin kasar Gahana, Accra yayinda daga nan kuma zasu karasa birnin Kumasi, inda a nan ne za’a buga wasan.

“Yan wasa da masu koyarwa da likitoci da kuma duk wadanda suke taimkawa kungiyar zasu tashi domin zuwa jihar Kaduna inda zasu kafa sansani a kokarin da mukeyi na ganin mun samu nasara a wasanmu na biyi” in ji shugaban kungiyar Surajo Yahaya

Ya cigaba da cewa “Muna fatan zamu samu nasara  a wasanmu na gaba saboda haka yakamata mu manta da sakamakon wasan farko na 3-2 mu mayar da hankali akan wasa na biyu wanda muke fatan zamu basu mamaki”

Kano Pillars dai tana bukatar canjaras kuma ta samu nasara idan har tana fatan sake zuwa zagaye na gaba inda zata fafata da kungiyar kwallon kafa ta Ettoile De Sahel ta Tunisia ko kuma Hiafa ta kasar Guinea.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!