Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Binuwe: Manomi Ya Gurfana A Kotu Bisa Kashe Abokinsa Da Wuka

Published

on

A ranar Litinin ce, wani manomi mai suna Terseer Angbee, ya gurfana a gaban kotun Makurdi, bisa laifin daba wa abokinsa wuka har lahira, inda zai cigaba da zama a gidan yari har sai an samu shawarwari daga ma’aikatar shari’a ta jihar. Alkali mai shari’a J. O. Ayia shi ne ya bayar da wannan umurni, inda ya yi watsi da duk wata shaida da Mista Angbee ya bayar a gaban kotu. Alkali mai shari’a Mista Anyia ya bai wa ‘yan sanda umurnin a kan su mika fayal ndin wannan shari’a ga ma’aikatar shari’a ta Jihar Benuwe, domin samu shawarwari. Ya kuma dage sauraron wannan kara har sai zuwa ranar 26 ga watan Agusta.

Tun da farko dai lauya mai gabatar da kara Godwin Ato, ya bayyana wa kotu cewa, wani mutum mai suna Mista Torngu Mwaikyoga da ke zaune a yankin Tse Agu Mbajor Tombo shi ne ya kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yan sanda da ke yankin Buruku. Mista Ato ya na zargin Mista Angbee da daba wa mahaifin wanda ya kai korafi mai suna Mwaikyoga Yandeb wuka, lokacin da gardama ya kaire tsakanin wanda a ke zargi da kuma mamacin, sakamakon tumbuke wasu bishiyoyin laimu da wanda a ke tuhuma ya yi. Mamacin daa ya mutu daga baya ne a babbar asibitin Buruku, sakamakon raunin wuka da ya samu.

Lauyan mai gabatar da karar ya bayyana cewa, wanda a ke tuhumar ya amsa laifin sa ne bayan da a ka gudanar da cikakken bincike. Ya kara da cewa, wannan laifi dai ya saba wa sashe na 222 na dokar fanal kot ta Jihar Benuwe ta shekarar 2004.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!