Connect with us

LABARAI

An Yi Garkuwa Da Diraba Da Fasinjoji 10 A Hanyar Abuja

Published

on

Al’ummar garin Ajowa Akoko ta Jihar Ondo sun fada cikin firgici a bisa zargin sace wani direban motar haya tare da fasinjojin motar masu zuwa Abuja guda 10 wanda wasu ‘yan bindiga suka sace su.

An bayar da rahoton cewa an sace su ne a kan babbar hanyar Obajana zuwa Abuja da ke Obajana, Jihar Kogi.

Mamallakin motar bas din da aka sace direban motar da fasinjojin, Mista Abdulganiyu Hakeem, ne ya kai kukan faruwar hakan.

Hakeem ya ce motar ta taso ne daga Ajowa Akoko, inda kuma ‘yan bindiga suka tsare ta a kan babbar hanyar suka kuma sace direban da fasinjojin motar suka yi cikin daji da su. ya kara da cewa, har zuwa makon da ya gabata ba a sami wata duriyar su ba, kusan mako guda da faruwar lamarin.

“An kuma ba mu labarin cewa baccin su ma an sace sama da fasinjoji 30 daga wasu motocin a lokacin farmakin da aka kai ma su a wannan lokacin.”

A cewar sa, “’Yan bindigar sun tuntubi iyalan wasu daga cikin wadanda suka sace din, inda suke neman a biya diyyar naira 200,000 domin fansar direban motar, sannan a biya fansar naira 100,000 domin a fanshi kowane guda daga cikin fasinjojin kafin a sako su.

An bayar da rahoton cewa tuni har iyalan mutanan da aka sace din sun fara tattara kudaden domin ganin sun fanso ‘yan’uwan na su daga hannun ‘yan bindigar.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na Jihar ta Ondo, Femi Joseph, cewa ya yi abin ya faru ne a wajen da ba cikin ikon sa ne ba, a lokacin da wakilin mu ya tuntube shi.

Joseph ya yi nuni da cewa, “Tun da dai ba a cikin Jihar Ondo ne lamarin ya auku ba, an dai kai rahoton aukuwar lamarin ga rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kogi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: