Connect with us

RIGAR 'YANCI

Gwamnatin Nasarawa Ta Rantsar Da Kwamitin Mutum 13

Published

on

Gwamnatin jihar Nasarawa ta rantsar da keamitin mutane 13, wadanda za su rika sa-ido kan harkokin kasuwanci a jihar. Gwamnatin ta ce dai mutanen za su rinka aiki ne dan ganin harkar kasuwanci ya habaka cikin ihar.

Da ya ke jawabi wajen taron bunkasa harkokin kasuwanci wanda ya gudana  a zauren taro na Ta’al da ke garin Lafia. Babban bako Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo

Yace; babu abinda yakai harkan kasuwanci mahimmanci a cikin alumma. Yace; harkan kasuwanci kowa zaka tarar yana kokarin tabawa.

Manyan ma’aikatan Gwamnati da yan siyasa dama mata masu zaman gida. Yace; harkane mai albarka zakaga an tashi daga wani kasa zuwa wani kasa domin gudanar da harkan kasuwanci.

Babu abinda zai daga darajar kasar mu da manyan biranai face kasuwanci.

Yayi kira ga alumman jihar Nasarawa dasu rungumi harkan kasuwanci saboda yana daga darajar gari. Sanan yayi kira ga matasa maza da mata kada mutum ya rena sana’ar da yakeyi saboda wanan shine mar tabar shi.

Lokacin da ya ke  bayani gaban dubban alumma tare da mukaddashin Shugaban kasa Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule (Barayan Lafia) yace harkan kasuwanci harkace da take habbaka kasa ba ki daya.

Saboda ta hanyar kasuwanci ne kowata Gwamnati take samun kudaden shiga da takeyiwa jama’a aiki na raya kasa.

Kowata kasa tana alfahari da hanyoyin kasuwanci da alumman ta ke gudanarwa. Gwamnan ya kara da cewa Akwai hanyoyi da dama da jihar Nasarawa zata bunkasa ta fuskacin kasuwanci.

Hanyoyin hakar ma’adinai da suke karkashin kasa zai iya gina jihar Nasarawa ta harkan cigaban kasuwanci. Jihar tana da albarkatun kasa mai tarin yawa wanda idan aka samu damar yin mu’amala da yan kasuwa zasu sarafa abubuwa da dama.

Alumman jihar Nasarawa maza da mata suna da rawar da zasu taka a harkokin kasuwanci. Masamman masu kananan sana’o’in dama manyan yan kasuwa da masu sarafa kayayakin gona ta hanyar gudanar da abinchi na gida.

Gwamnan yayi kira ga masu gudanar da kananan sana’o’i da su zage dantse wajen gudanar da ayyukan su saboda gaba zasuyi murna da farin ciki.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: