Cibiyar hana yaduwar cutttuka da maganainsu ta kasa ta bayyana cewa a shekarar 2022 da ta gabata mutane 23,550 suka kamu da cutar kwalara, yayin da 583 suka rasa rayukansu a jihohi 32 da Babban Birnin Tarayya Abuja daga watan Janairu zuwa Nuwamba na shekarar 2022 da ta gabata.
Rahoton ya bayyana cewa cutar ta shafi jihohi 32 da suka hada da Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benuwai, Borno, Kuros Ribas, Delta, Ekiti, Abuja, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Legas, Nasarawa, Neja, Ondo, Osun, Oyo, Filato, Ribas, Sakkwato, Taraba Yobe da kuma Zamfara.
Har ila yau, rahoton ya nuna cewa jihohi shida da suka hada da Borno, Yobe, Katsina, Gombe, Taraba da Kano suke da kashi 84 na dukkan wadanda suka kamu da cutar a kananan hukumomi 15, kowannensu ya ba da bayanai kan fiye da mutane 200 da suka kamu da cutar.
Haka nan ma rahoton ya nuna a watan Nuwamba na shekarar da ta gabata, jihohi shida sun ba da bayanin mutane 1,393 sun kamu da cutar kamar, wanda ya nuna cewa Borno 1124, Gombe 165, Bauchi 61, Katsina 16, Adamawa 14, sai kuma Kano 13.
Sai dai kuma duk da hakan rahoton ya bayyana samun koma-bayan na wadanda suka kamu da cutar a cikin sabbin alkalumma a watan Nuwamba an samu kashi 78, ba kamar watan Oktoba ba da ake da mutane 6306.