Ɗan takarar shugabancin ƙasa a PDP, ya yi alwashin fara sauya fasalin Nijeriya daga ranar da ya zama shugaban ƙasa a 2023, idan ya yi nasarar lashe zaɓe.
Wazirin Adamawa ya yi wannan alwashin a Osogbo, babban birnin Jihar Osun, lokacin kamfen ɗin PDP a jihar.
Ya ce zai yi amfani da ajandar sa ta sauya fasalin Nijeriya domin ya kawo ƙarshen matsalar tsaro da sauran ƙalubalen da ƙasar nan ke fama da fuskanta.
Ya ce daga lokacin da aka gama rantsar da shi zai fara aiwatar da ayyukan raya ƙasa ta hanyar sake fasalin Nijeriya.
“Babban muradin mu shi ne mu tabbatar mun kawar da dukkan matsalolin rashin tsaro, rarrabuwar kawuna, kawar da danne haƙƙin tallalin arzikin jama’a da samar da aikin yi ga matasa. Ina ɗaukar maku alƙawarin cewa tun daga ranar da aka naɗa ni shugaba idan na yi nasara a zaɓen 2023, zan aiwatar da su,” inji Atiku.
Daga nan sai ya roƙi al’ummar jihar Osun su jefa masa ƙuri’un su, domin ya cimma burin sa na ceto Najeriya daga mawuyacin halin da ya ce mulkin APC ya jefa ƙasar.
“Ba za mu kunyata ku ba, kuma ba za mu ci amanar ku kamar yadda APC ta ci amanar ku ba. Saboda mu na da ƙwarewa da irin gogewar da Najeriya ke matuƙar buƙata.”
Gwamna Ademola Adeleke, wanda aka rantsar kwanan nan, ya bayyana Atiku Abubakar a matsayin gogagge kuma mai ƙwarewar da zai iya ceto Nijeriya, har ya magance matsaloli da ƙalubalen da su ka dabaibaye ƙasar.