Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana jam’iyyar APC a matsayin wadanda suka rusa Nijeriya, ya kara da cewa basu cancanci a basu goyon baya ba.
Atiku, ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar a Benin, babban birnin Jihar Edo, a ranar Asabar a wajen taron gangamin jam’iyyarsa na shugaban kasa, ya bukaci jama’a su ci gaba da kasancewa masu biyayya ga PDP.
- Kasar Sin Na Adawa Da Yin Shisshigi Cikin Harkokin Gidan Kasashe Masu Tasowa Bisa Hujjar Kare Hakkokin Dan Adam
- Taron Wakilan Jam’iyyar Kwaminis Ta Kasar Na 20 Da Muhimmancinsa
Ya ce jam’iyyar APC ta lalata tsarin ilimi, tattalin arziki, ababen more rayuwa da kuma kasa magance matsalolin tsaro da kasar nan ke fuskanta.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma jaddada aniyarsa na magance matsalar rashin tsaro, inganta tattalin arziki, hada kan kasa da yaki da rashin tsaro.
Atiku ya ce “Mun yi alkawarin sake hade kasar nan. Me muke nufi da haka? Muna nufin za mu bai wa kowane bangare na kasar nan dama. Ba za a cire ku a cikin komai ba.
“Na biyu, mun yi alkawarin dawo da tsaro. Za mu dawo da tsaro a kasar nan, ta yadda za ku yi tafiya dare da rana, domin ku je gonakinku, ta yadda za ku je ko’ina cikin tsari.
“Za mu sanya ‘yansanda da yawa a kan tituna. Za mu ba su kayan aiki; za mu karfafa musu kuma tun da mun yi alkawarin ba da karin iko ga jihohi da kananan hukumomi, za ku iya samun ‘yansanda na yankinku. Za mu tabbatar da cewa ‘yansandan yankinku ba su tursasa ku ba.
“Na uku, za mu mayar da dukkan yaranmu da suka cancanta makaranta. Dole ne su je makaranta; dole ne kowane yaro ya je makaranta.
“Idan za ku tuna, a shekarun PDP mun kafa ilimin firamare na tilas tun daga firamare zuwa sakandare kuma muna daukar nauyin ‘yan Nijeriya da su ilimantar da wadannan yara. Amma wannan gwamnati ba ta cika wannan alkawari ba. Mun yi muku alkawari; dole ne kowane yaro ya je makaranta kuma jami’o’inmu ba za su tafi yajin aiki ba.
“Haka kuma, mun yi alkawarin farfado da tattalin arzikin kasar nan. Za mu tabbatar da cewa masana’antunmu sun dawo da samar da kayayyaki a kasar nan. Za mu tabbatar da samar da isassun ayyukan yi ga matasanmu da ke fita waje makarantu. Wannan shi ne abin da muke nufi da farfado da tattalin arziki.
“Kun ga yadda APC ta lalata kasar nan, ta lalata tattalin arzikin kasar nan. Sun lalata damar karatunku. Sun lalata muku damar aikinku. APC ba jam’iyyar da za a goya wa baya ba ce. Sun lalata komai.
“Saboda haka, muna kira a gare ku da ku ci gaba da yin biyayya ga PDP kuma PDP za ta kasance mai biyayya gare ku.”