Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa jam’iyyar APC za ta lashe zaben shugaban kasa cikin ruwan sanyi a 2023.
Buhari ya ce APC ta yi sa’ar samun Tinubu a matsayin dan takararta na shugaban kasa.
- Hadin Gwiwar Sin Da Afrika Kan Tattalin Arzikin Zamani Ya Baiwa Afrika Damammaki Masu Kyau
- Gwamnatin Kaduna Ta Karyata Rahoton Kai Hari A Hanyar Kaduna-Abuja
Ya yi wannan maganar ne a Birtaniya yayin da yake mayar da martani kan yiwuwar APC ta lashe zaben shugaban kasa a 2023.
Da aka tambaye shi kan yiwuwar APC na rashin yin nasara a 2023, Buhari ya ce: “Mene ne zai hana jam’iyyata ta ci zabe? Za mu ci zabe.
“Tinubu, dan takarar shugaban kasa, sanannen dan siyasa a kasar nan, ya yi gwamna har biyu a Jihar Legas, jihar da ta fi kowace arziki kuma jihar da aka fi ziyarta.
“Don haka, ina ganin jam’iyyar ta yi sa’ar samun shi a matsayin dan takara.”
A watan Yuni, Tinubu ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC bayan ya doke mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi.
Tsohon gwamnan Jihar Legas ya samu kuri’u 1,271 inda ya doke abokin hamayyarsa Amaechi wanda ya samu kuri’u 316.
Bayan zamansa dan takarar jam’iyyar, wasu badakaloli da dama sun biyo bayan sahihancinsa na mulkin Nijeriya.
Duk da wadannan zarge-zargen, kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa ta jam’iyyar APC ta wanke Tinubu daga duk wani ikirarin da ake yi a kansa.