Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da ka da su sake zabar jam’iyyar APC a zaben 2023.
Atiku, ya yi wannan kiran ne cikin sanarwar da kakakin PDP a Jihar Sakkwato, Hassan Sanyinnawal, ya fitar, inda ya ce, Atiku ya yi gargadin ne a jawabin da ya yi a taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a Jihar Kano.
- Ba Zan Bari Kowa Ya Kawo Cikas A Zaben 2023 Ba – Buhari
- Yanzu-yanzu: Tinubu Ya Gana Da Jonathan, Ya Nemi Ya Mara Masa Baya
Atiku ya ce idan ‘yan Nijeriya suka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2023, zai magance kalubalen rashin tsaro, hauhawar farashin kayan masarufi, inganta fannin ilimi da sauransu.
A cewarsa, APC ta rasa inda za ta fuskanta da yin tunani kan yadda za ta lalubo da mafita kan matsalolin da Nijeriya ke ci gaba da fsukanta, inda ya yi nuni da cewa, hakan ya nuna a zahiri, APC ta gaza.
Shi ma a nasa jawabin, shugaban kungiyar gwamnonin PDP, gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayar da tabbacin cewa, nasara na tare da PDP a daukacin jihohi bakwai da ke a yankin na Arewa Maso Yamma.
Tambuwal ya ce APC ba ta da wata hujjar sake yi wa ‘yan Nijeriya kamfen ganin cewa ta gaza, inda ya ce duk mai tunani ba zai sake zabar APC ba.
Wasu daga cikin mahalarta taron, su ma sun gargadi ‘yan Nijeriya kan sake zabar APC a zaben 2023, musamman inda suka danganta irin halin kuncin rayuwa da APC ta jefa ‘yan Nijeriya a ciki.