Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana ƙudirinsa na ƙara wa gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi ƙarfin gudanar da mulkinsu idan an zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a watan gobe.
Atiku ya faɗi haka ne a taron yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar wanda aka yi a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, a ranar Alhamis.
A jawabinsa kan shirin da ya yi wa ƙasar nan a wajen taron, wanda aka yi a Zauren Mapo, Atiku ya ce a ƙarƙashin gwamnatinsa za a sake fasalin mulkin ƙasar nan ta yadda za a tabbatar da cewa an ƙara wa gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi ikon gudanar da mulki.
Ya ce, “An san mutanen yankin Kudu-maso-yamma da neman a sauya fasalin ƙasar nan. Idan an ce sauya fasali, muna nufin a ba da ƙarin ikon mulki ga jihohi da ƙarin kuɗi. Ko kun fahimci hakan? Ko kun amince da a yi hakan?
“Yana daga cikin ginshiƙai biyar na shirye-shiryenmu don mu aiwatar da sauyin fasalin ƙasar nan — manufa ita ce mu ba ku ƙarin kuɗi da ƙarin ikon mulki ta yadda za ku iya haɓaka yankunan ku da jihohin ku da ƙananan hukumomin ku. Wannan shi ne mu ka sa a gaba.
“Haka kuma, mun ƙudiri aniyar tabbatar da ba za a ƙara yin yajin aiki a jami’o’in mu ba — manufa za mu ba jami’o’in mu isassun kuɗi tare da biyan malaman mu a kan lokaci ta yadda ba za mu samu wani cikas a harkokin ilimin mu ba.
“Tilas mu tabbatar da cewa mun rungumi kowa da kowa. Kowane ɓangare na ƙasar nan zai samu wakilci a gwamnatin mu.
“Haka kuma mun ƙudiri aniyar tabbatar da mun samar da tsaron ƙasar mu don tabbatar da an samu kwanciyar hankali, tare da bin doka da oda a kowane ɓangare na ƙasar nan. Wannan shi ne abin da mu ka ƙudirta.”
Bugu da ƙari a jawabin nasa, Atiku ya yaba wa Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo kan yadda ya tabbatar da cewa taron yaƙin neman zaɓen ya shiryu sosai.
Duk da yake gwamnan bai halarci taron ba, Atiku ya ce, “Jama’ar Jihar Oyo, bari in yi amfani da wannan damar in ƙara yin godiya ga Gwamna Makinde da jam’iyyar PDP reshen Jihar Oyo saboda yadda su ka tabbatar da cewa wannan taron ya shiryu matuƙa kuma an yayata shi sosai.”
Shi ma Shugaban PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, wanda ya yi jawabi a wajen taron, ya yaba wa Makinde saboda “nasarar da aka samu” a wajen kamfen ɗin jam’iyyar a jihar.
Makinde dai ya na cikin gwamnonin nan na PDP guda biyar waɗanda ake kira G5, wato waɗanda su ka ware kan su daga kamfen ɗin da Atiku ke yi a faɗin ƙasar nan.
Sun yi hakan ne bisa kasa samun biyan buƙatar su ta lallai sai Ayu ya yi murabus daga kujerar sa ta shugaban jam’iyyar na ƙasa.
Gwamnonin su ne Nyesom Wike na Ribas, Ifeanyi Ugwuanyi na Inugu, Samuel Ortom na Binuwai, Seyi Makinde na Oyo, da Okezie Ikpeazu na Abiya.