Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi watsi da rade-radin da wasu ke yadawa cewar, idan ya zama shugaban kasa a 2023, zai mayar da Babban Birnin Tarayyar kasar nan zuwa Jihar Legas.
Tsohon shugaban kasa na mulkin soji Ibrahim Babangida ne, ya dawo da birnin tarayyar kasar nan daga Jihar Legas zuwa Abuja a rnar 12 ga watan Disambar 1991.
- Gwamnatin Kebbi Ta Zargi Aliero Da Wasu Kan Yi Wa Jihar Zagon Kasa Kan Wasu Ayyuka
- Sin: Ya Kamata Amurka Ta Dakatar Da Mayar Da Batun Ciniki Da Kimiyya A SiyasanceÂ
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da daraktan yada labarai na kwamitin yakin neman zaben dan takarar APC na shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar a madadin Asiwaju.
Sanarwar ta nesanta kanta da wannan batun, inda kwamitin ya ce, “Kwamitin yakin neman zaben na son ya sanar da ‘yan Nijeriya cewa, Asiwaju bai da wani shirin mayar da babban birnin tarayyar kasar nan zuwa Jihar Legas idan ya zama shugaban kasa a 2023.
Sanarwar ta ce, “Yarfe ne kawai na siyasa da jam’iyyun PDP da LP suka kitsa don bata wa Asiwaju suna, inda sanarwar ta kara da cewa, a cikin irin wadandan karairayin da suke yada wa, mussaman a Arewa maso yamma sun ce, Asiwaju da zararar ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari daga ranar 29 ga watan Mayun 2023, zai mayar da babban birnin tarayyar Abuja zuwa Jihar Legas.
A cewar sanarwar, wasu ‘yan barandar jam’iyyar PDP ne ke kitsa wannan labaran na kanzon kurege a kan Asiwaju, inda sanarwar ta kara da cewa, ta yi matukar mamaki a kan yadda irin wadandan mutanen suke yada karya duk da sunan siyasa.
Sanarwar ta ce, duk dai irin wadandan mutanen ne ke rikitar da shirin sayar da hannun harin kamfanin NNPC, inda sanarwar ta yi nuni da cewa, maganar gaskiya, Buharibbai satar da hannun jarin NNPC karin ba kamar yadda Atiku ke shirin yi.
A cewar sanarwar, a maimakon sayar da hannun harin kamfanin, Buhari ya mayar da kamfanin ne yadda daukacin matakan gwamnati uku za su mallaki kamfanin daidai da dokar masana’antar mai.
Sanarwar ta ce, Asiwaju in ya zama shugaban kasar, zai ci w da ayyukan da gwamnatin Buhari ta faro, sabanin Atiku da ke da kudin sayar da NNPC ga abokansa kadai.