A daren ranar Laraba Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, ya gana da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin sadarwa na zamani, Bashir Ahmad, ya tabbatar da hakan a shafin sa na Twitter.
- Qatar 2022: Babban Bankin Argentina Na Kokarin Sanya Hoton Messi A Takardun Kudin Kasar
- Kotu Ta Ba Da Umarnin Kwace Dala 899,900 Da Naira Miliyan 304 A Wurin Ahmed Idris
Ahmad ya ce: “Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin dan takararmu na shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a safiyar yau, a gidansa da ke fadar shugaban kasa, Abuja.”
A baya dai Buhari ya bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya tabbatar wa jam’iyyar APC da ‘yan takararta cewa zai tabbatar da nasarar zaben shugaban kasa da sauran ‘yan takarar jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.
Buhari ya ce a shirye yake a kowane lokaci don yin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa da kuma dukkan ‘yan takarar jam’iyyar da “cikin kuzari da yakini”.
Shugaban ya bayyana cewa an ba da wannan tabbacin ne domin kawar da damuwar da wasu ke nunawa cewa ba ya zuwa ana yakin neman zaben jam’iyyar, tun bayan kaddamar da yakin neman zaben jam’iyyar a garin Jos na Jihar Filato.
Sai dai ya jaddada cewa duk da yake ya tsaya tsayin daka kan siyasar jam’iyya da ayyukan shugaban kasa amma zai taimakawa jam’iyyar.
A baya dai mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya kai wa Tinubu ziyara a gidansa da ke Abuja a ranar Laraba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp