Bayani ya nuna cewa, shekarar 2023 ta zo da armashi ga banaren harkokin inshora da masu zuba hannun jari a inda masu zuba jari suka samu ribar fiye da Naira Tiriliyan 11.7 yayin da masu harkar inshora suka tashi da ribar fiye da na naira tiriliyan 1, kamar yadda jaridar LEADERSHIP Sunday ta nakalto mana.
Wannan yana faruwa ne duk da tsananin matsalolin tattalin arzikin da ake fuskanta wanda ya yi sanadiyyar mutuwa manya da kananan kamfanoni da dama ya kuma yi sanadiyyar ficewa wasu manyan kamfanoni daga Nijeriya.
Kasuwar hannun jari ta samu ribar naira tiriliyan 11.734 a daidai ranar 14 ga watan Disamba na wannan shekarar 2023, ana kuma da fatan dorewar wannan nasarar har zuwa karshen shekara da farkon shekara mai kamawa.
Tun da farkon wannan shekarar an lura da bunksar kasuwar hannun jari inda masu sayen hannayen jari suka karu suna kuma sayen hanun jari masu yawan gaske.
Ribar hannun jarin da aka samu ya tashi daga Naira tiriliyan 11.734 zuwa naira tiriliyan 27.915 a farkon shekarar 2023 zuwa Naira Tiriliyan 39.649 a daidai ranar 14 ga watan Disamba na shekarar 2023.
Haka kuma kudin hadahadar musaya a Nijeriya ya tashi da kashi 41.37 daga maki 51,251.06 a ranar 30 ga watan Disamba 2022 zuwa maki 72,455.83 a daidai ranar 14 ga watan Disamba 2023.
Shugaban kamfanin harkar hannun jari mai suna Mike Ezeh, ya bayyana cewa, bayyanar Shugaba Tinubu a mastayin shugaban kasa ya taimaka wajen farfado da kasuwar hannun jari a Nijeriya, musamman yadda zaben 2023 ya zo ba tare da wasu rikice-rikice ba, wadannan ne suka bai wa masu zuba jari kwarin gwiwa da sake jiki wajen sayen hannun jari a Nijeriya.
Haka kuma bangaren inshora ya samu ribar Naira biliyan 729.1 a zango na uku na wannan shekarar an kuma yi hasashen zai iya kaiwa tiriliyan 1 a zango na farfro na shekara mai kamawa, in har haka ya faru kuwu zai kasance kenan a karon farko da ake samu irin wannan ci gaban a cikin shekara 8.
‘Yan Nijeriya sun ci gaba da yankar inshorar rayuwa (Life Insuarance) musamman ganin matsalolin rashin tsaro don iyalansu su samu abin rufa wa kansu asiri in sun mutu, an tabbatar da cewa, iyalai sun kashe naira biliyan 265.39 a yankar inshorar rayuwa a cikin wata 9 duk kuwa da matsalolin tattalin arzikin da ake fuskanta.