Jimlar bashin da ake ci a gida Nijeriya ya tashi da kashi 133.95 inda ya kai zuwa Naira tiriliyan 51.96 a karshen shekarar 2023.
Bayanin hakan ya samo asali ne daga sabbin bayanan da Darakta Janar na Ofishin Kula da Bashi (DMO), Patience Oniha ta yi.
- Majalisar Dokokin Sokoto Ta Amince Da Bukatar Gwamna Aliyu Na Kafa Jami’an Tsaron Jiha
- Lokaci Ya Yi Da Za A Mayar Da Kayayyakin Tagulla Na Daular Benin Gida
Ta bayyana hakan ne a yayin da take jawabi a wurin taron tattaunawar kafa cibiyar kula da basussuka ta Afirka da bankin raya Afirka ke jagoranta a Abuja.
Ta ce gwamnatin tarayya ta tara naira tiriliyan 7.04 a matsayin sabbin bashin cikin gida a 2023.
Oniha ta ce, “Na yi farin cikin cewa a shekarar 2023, sabon bashin cikin gida ya kai na naira tiriliyan 7.04, kuma a lokacin da muke magana an samu ci gaba. Don haka, ba na bukatar in yi bayyana yadda muka tayar da shi, amma an tashe shi. Idan aka kwatanta shi da na naira tiriliyan 3.5 na bara. Wannan na nuna maka cewa kasuwa na da tulin bashi don mu tara kudi.”
Zuwa karshen watan Disambar 2022, jimillar bashin da ake bin Nijeriya ya kai na naira tiriliyan 22.21. Hakan ya karu sosai a karshen watan Yuni wanda ya kai na naira tiriliyan 48.32.
DMO ya bayyana cewa, babban abin da ya janyo karuwar basussukan shi ne, saka naira tiriliyan 22.71 da gwamnatin tarayya ta amince da shi wanda ke bayyana a cikin bashin cikin gida.