• English
  • Business News
Saturday, August 30, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2023: Matukar Mutum Ba Shi Da Katin Zabe Ba Zai Jefa Kuri’a Ba – INEC

by Sulaiman
3 years ago
in Labarai
0
2023: Matukar Mutum Ba Shi Da Katin Zabe Ba Zai Jefa Kuri’a Ba – INEC
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta shawarci duk wanda ya san ya yi rajistar zaɓe, to ya gaggauta zuwa karɓar katin shaidar rajistar sa PVC, domin babu wanda za a bari ya yi zaɓen 2023 ba tare da katin rajista ba.

Kwamishinan INEC na Jihar Katsina, Farfesa Ibrahim Yahaya Maƙarfi, shi ne ya jaddada haka a cikin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a ranar Lahadi a Katsina.

  • 2023: INEC Ta Gargadi Masu Sayar Da Katin Zabensu Ga ‘Yan Siyasa

Ya ce hukumar ba za ta bai wa wani uzirin yin zaɓe ba tare da katin shaidar rajista ba.

Labarai Masu Nasaba

Babban Taron Lauyoyi Na Kasa: Sarkin Musulmi Ya Gargadi Alkalai Kan Tabbatar Da Adalci

Cire Tallafin Wutar Lantarki Zai Kara Kuntata Rayuwar ‘Yan Nijeriya – Kungiyar Kwadago

Ya ce INEC ta dakatar da ci gaba da rajistar masu zaɓe tun a ranar 31 ga Yuli, saboda tilas sai an ɗauki lokaci ana tattarawa, tantancewa da kuma taskace sunaye da bayanan waɗanda aka yi wa rajistar, kafin a kai ga buga wa kowa katin rajista.

Maƙarfi ya ce ta wannan tsarin ne INEC ke wa masu zaɓe rajistar da za ta ba su damar zaɓen duk wani ko wata ‘yan takarar da su ke so su zaɓa.

Ya ce: “Sashe na 16(1) na Dokar Zaɓe ya wajibta wa INEC yi wa masu zaɓe rajista, buga katin rajista da kuma damƙa wa duk wanda ya yi rajista katin sa a hannu. Amma tilas sai wanda sunan sa ya fito a jerin sunayen da ke cikin rajista kaɗai za a iya bai wa katin zaɓe.

“Ya na da kyau a san cewa katin shaidar rajista shi ne shaidar amincewa mutum ya yi zaɓe, kamar yada Sashe na 47 na Dokar Zaɓe ta 2022 ya tanadar.

“Daga ranar 12 ga Disamba INEC za ta fara raba katin shaidar rajistar zaɓe, har zuwa ranar 22 ga Janairu, 2023.

“Za mu raba katin a dukkan ƙananan hukumomi 34 na jiha, kuma za a koma ana rabawa a dukkan cibiyoyin rajistar zaɓe 361 na jiha daga ranar 6 zuwa 15 ga Janairu, 2023.”

INEC ta yi kira ga duk wanda ya san ya yi rajista ya je ya karɓi katin sa. Hukumar ta ƙara yin sanarwar cewa za a riƙa raba katin tun daga ƙarfe 9 na safe har zuwa 3 na yamma, a kullum har da ranakun Asabar da Lahadi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

An Kafa Dokar Hana Shan Sigari A New Zealand

Next Post

Yadda Dangin Ango Da Amarya Suka Bai Wa Hammata Iska Kan Sadaki 

Related

Gidauniyar ‘Ya’yan Sarakunan Arewa Sun Marawa Sarkin Musulmi A Matsayin Shugaban Majalisar Sarakuna
Rahotonni

Babban Taron Lauyoyi Na Kasa: Sarkin Musulmi Ya Gargadi Alkalai Kan Tabbatar Da Adalci

7 hours ago
Sin Ta Fara Amfani Da Tauraron Dan Adam Wajen Duba Manyan Hanyoyin Wutar Lantarki A Karo Na Farko
Rahotonni

Cire Tallafin Wutar Lantarki Zai Kara Kuntata Rayuwar ‘Yan Nijeriya – Kungiyar Kwadago

9 hours ago
Legas Ta Laƙume Aikin Naira Tiriliyan 3.9 Cikin Shekaru Biyun Tinubu
Manyan Labarai

Legas Ta Laƙume Aikin Naira Tiriliyan 3.9 Cikin Shekaru Biyun Tinubu

9 hours ago
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas
Tsaro

‘Yansanda Sun Ceto Wani Dan Shekara 25 Da Aka Sace A Jihar Kebbi

11 hours ago
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi
Tsaro

An Cafke Mutum Hudu Bayan ‘Yan Fashi 20 Sun Afka Wasu Gidaje A Bauchi

12 hours ago
NDLEA Ta Kama Wani Matashi Dan Shekara 29 Da Kwayoyin Tramadol 7,000 A Kano
Tsaro

NDLEA Ta Kama Wani Matashi Dan Shekara 29 Da Kwayoyin Tramadol 7,000 A Kano

13 hours ago
Next Post
Yadda Dangin Ango Da Amarya Suka Bai Wa Hammata Iska Kan Sadaki 

Yadda Dangin Ango Da Amarya Suka Bai Wa Hammata Iska Kan Sadaki 

LABARAI MASU NASABA

Shugaban Kasar Sin Ya Gana Da Firaministan Kasar Masar

Shugaban Kasar Sin Ya Gana Da Firaministan Kasar Masar

August 30, 2025
Ranar Hausa: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka

Ranar Hausa: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka

August 30, 2025
Xi: Har Kullum Sin Za Ta Kasance Amintacciyar Abokiyar Huldar MDD

Xi: Har Kullum Sin Za Ta Kasance Amintacciyar Abokiyar Huldar MDD

August 30, 2025
Gyaran fuska

Gyaran Fuska Da Laushin Fata

August 30, 2025
Shugaban Belarus Ya Jinjinawa Gudummawar Sin A Fannin Inganta Ci Gaban Kungiyar SCO

Shugaban Belarus Ya Jinjinawa Gudummawar Sin A Fannin Inganta Ci Gaban Kungiyar SCO

August 30, 2025
majalisar kasa

Tarihin ‘Yan Majalisar Farko A Nijeriya Kafin Zamanin Mulkin Mallaka

August 30, 2025
Sin Da AU Sun Sabunta Hadin Gwiwa Game Da Bunkasa Amfani Da Fasahohin Zamani Wajen Raya Noma A Afirka

Sin Da AU Sun Sabunta Hadin Gwiwa Game Da Bunkasa Amfani Da Fasahohin Zamani Wajen Raya Noma A Afirka

August 30, 2025
Yadda Jariri Ke Koyon Tsotsar Nonon Uwa Kafin Haihuwa

Yadda Jariri Ke Koyon Tsotsar Nonon Uwa Kafin Haihuwa

August 30, 2025
Sin Da Amurka Sun Yi Musayar Ra’ayoyi Game Da Batutuwan Cinikayya

Sin Da Amurka Sun Yi Musayar Ra’ayoyi Game Da Batutuwan Cinikayya

August 30, 2025
Lambar Yabo Ta CON: Buni Ya Zama Zinare Bashi Da Maboya

NTIC Ta Jinjina Wa Gwamna Buni Kan Taimako A Bangaren Ilimi

August 30, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.