Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta ce dukkan ma’aikatan wucin-gadin da za ta ɗauka sai sun yi rantsuwar cewa ba za su nuna goyon bayan kowace jam’iyyya ba, kuma ba za su nuna goyon baya kan kowane ɗan takara ba.
Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke duba irin horaswar da ake bai wa wasu jami’an gudanar da zaɓe.
Ya ce tilas su yi rantsuwar tun kafin a tura kowanen su wurin da zai je ya yi aikin zaɓe.
Yakubu ya ce dukkan ma’aikatan INEC na dindindin da na wucin-gadi ɗin, duk Najeriya da ‘yan Najeriya su ke yi wa aiki, ba wata jam’iyya ko ɗan takara ba.
Yakubu ya shaida masu cewa yayin da INEC ta ƙudiri aniyar gudanar da sahihi kuma karɓaɓben zaɓe wanda ba a taɓa yin kamar sa ba a tarihin zaɓukan Nijeriya na baya, ya ƙara da cewa gaskiya da ƙimar ma’aikatan zaɓe ce za ta yi wa zaɓen kyakkyawar shaida da tasiri.
Ya ce an yi taka-tsantsan sosai wajen tsamo ma’aikatan ne a tsanake bisa ga yin la’akari da wasu halaye da dalilai.
Ya ce a duniya babu wani shugaban hukumar zaɓe da ke iya gudanar da zaɓe ta hanyar amfani da ma’aikatan ofishin sa kaɗai. Ya ce wannan dalilin ya sa tilas INEC ke ɗaukar ma’aikata na wucin-gadi a lokacin zaɓe.