• English
  • Business News
Friday, October 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2023: Fitaccen Mawakin ‘Bauchi Sai Bala’ Ya Fice Daga Tafiyar Bala Ya Koma Mara Wa Sadiqu Na APC Baya

Ya Sauya Wakar Zuwa Bauchi Sai Sadique

by Khalid Idris Doya
3 years ago
2023

Fitaccen Mawakin gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad, wato Alhaji Ibrahim Sabo Mai Kukuma mai wake ‘Bauchi Sai Bala’ ya fice daga tafiyar Bala.

Mawakin ya shelanta goyon bayansa ga dan takarar Gwamnan Jihar na jam’iyyar APC, Air Marshal Sadique Baba Abubakar, a zaben 2023 da ke tafe.

  • Buhari Ya Halarci Wajen Kaddamar Da Hako Man Fetur A Bauchi 
  • Gwamnan Bauchi Ya Gabatar Da Kasafin Kudi Na Naira Biliyan 202.6 Na Shekarar 2023

A wani faifayin bidiyo da kuma hotunansa da aka nada tare da Air Marshal Sadique (mai ritaya) a wajen wani taron karbar wadanda suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a karamar hukumar Ningi, an gano da jiyo Mawakin na rera baitocin waken siyasa ga Sadiq.

Ita da wakar ‘Bauchi Sai Bala’ ta zama bakandamiyar wakar da PDP da gwamna Bala Muhammad suka yi amfani da ita a zaben 2019 wanda kuma har bayan kafa gwamnati ana yawan sanyata a wajen tarukan siyasa da na gwamnati wanda har ta kan sanya gwamna Bala fitowa ya dan takara rawa idan aka sanyata.

Wakar an mata zubin salo na fikira da basira wacce ake jero matsalolin da suke damun Bauchi da kuma kiran jama’a da su zabi Bala Muhammad a cikinta.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP

Kwamitin Shura Na Kano Ya Dakatar Da Malam Lawan Triumph Daga Yin Wa’azi

Kwatsam kuma sai a jiya mawakin ya sauya inda ya yi amfani da ita ga babban abokin takarar Gwamna Bala, wato Air Marshal na jam’iyyar APC a zaben 2023.

A cikin baitocin waken da wakilinmu ya ji tare da saurara cikin nutsewa, ya fahimci cewa kalmomi kusan iri daya mawakin ya yi amfani da su, illa kawai yanzu na kira da a zabi Sadiq da cewa ‘Bauchi Sai Sadik’.

Alhaji Sabo dai ya yi fice matuka wadda har aka canza masa suna zuwa mai wakar Bauchi sai Bala don haka fitarsa daga masoya da magoya bayan gwamna Bala ya zo wa jama’a da mamaki matuka.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP
Da ɗumi-ɗuminsa

Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP

October 15, 2025
Kwamitin Shura Na Kano Ya Dakatar Da Malam Lawan Triumph Daga Yin Wa’azi
Da ɗumi-ɗuminsa

Kwamitin Shura Na Kano Ya Dakatar Da Malam Lawan Triumph Daga Yin Wa’azi

October 1, 2025
NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025
Da ɗumi-ɗuminsa

NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025

September 17, 2025
Next Post
‘Yan Nijeriya Na Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Sabbin Takardun Kudin Da Aka Kaddamar

‘Yan Nijeriya Na Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Sabbin Takardun Kudin Da Aka Kaddamar

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

October 16, 2025
NAWIA

Ranar Abinci Ta Duniya: NAWIA Ta Tallafawa Mata 114  Da Kayan Aikin Gona A Zamfara

October 16, 2025
Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

October 16, 2025
Gaza

Wane Ci Gaba Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza Ta Haifar?

October 16, 2025
Tsohon Ɗan Wasan Dambe, Ricky Hatton Ya Rataye Kansa

Tsohon Ɗan Wasan Dambe, Ricky Hatton Ya Rataye Kansa

October 16, 2025
Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin

Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin

October 16, 2025
Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da Zai Taimaka Wajen Gwaje-wajen Kimiyya

Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da Zai Taimaka Wajen Gwaje-wajen Kimiyya

October 16, 2025
Tinubu

Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa

October 16, 2025
Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

October 16, 2025
Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

October 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.