Ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar, Wazirin Adamawa ya yi alƙawarin cewa zai mayar da hankalin sa wajen farfaɗo da harkokin ilmi tare da inganta shi, ya na mai zargin cewa, “gwamnatin APC ta kashe harkar ilmi a ƙasar nan, ta hanyar bijiro da tsare-tsaren da kowa ya san ba za su inganta ci gaban ilmi ba.”
Atiku ya bayyana haka ne a yayin ƙaddamar da fara kamfen ɗin sa na shiyyar Kudu maso Yamma a Akure, babban birnin Jihar Ondo cikin makon nan.
Daga nan ya ƙara jaddada irin alƙawarin da ya yi a Ilorin, wanda ya ce idan ya yi nasara, gwamnatin sa za ta ware dala biliyan 10 domin bunƙasa ƙanana da matsakaitan masana’antu, ta yadda matasa za su yunƙuro wajen samun aikin yi sosai, su ma mata rayuwar su za ta ƙara bunƙasa.
Da ya ke jawabi a wurin gangamin, wanda ya samu halartar ɗimbin magoya bayan PDP, Atiku ya ce Nijeriya ta yi asarar shekaru takwas da APC ta yi ta na mulki, wanda su ka jefa jama’a cikin mawuyacin halin da ba shi misaltuwa.
Ya yi fatan cewa, “daga 2023, kada Allah ya sake jarabtar ‘yan Nijeriya da irin mulkin APC.”
Kafin ya fara jawabi, sai da uwargidan sa Titi Abubakar ta fara yi wa dandazon magoya bayan PDP jawabi tukunna.
Titi, wadda haifaffiyar Jihar Ondo ce, ta ce ta yi farin cikin ganin PDP ta fara kamfen ɗin shiyyar Kudu maso Yamma a jihar ta ta haihuwa.
“Ina gabatar da kai na a gare ku, a matsayi na na ‘yar ku. Idan ku ka zaɓi miji na, zai daƙile Boko Haram kuma zai inganta ilmi.
“Kada ku manta, miji na ne ya yi nasara a zaɓen 2019, amma aka yi masa maguɗi, aka murɗe zaɓen. To kada ku bari a sake yaudarar ku. Wannan lokacin ma ku fito ku sake zaɓen PDP.
“Idan Atiku ya yi nasara, wata dama ce da Jihar Ondo za ta samu cewa ‘yar su za ta zama uwargidan shugaban ƙasa. Dama kuma Bayarabiya ba ta taɓa zama uwargidan shugaban ƙasa a Najeriya ba.”
Da ta ke yabon mijin ta, Titi ta ce ko lokacin da ya na mataimakin shugaban ƙasa ya yi rawar gani, domin shi ne ya janyo irin su Nasir El-Rufai da Ngozi Ikwenja-Ewela cikin gwamnati, “har da ma wasu fitattun haziƙan da su ka kawo ci gaba a ƙasar nan.
Mataimakin takarar Atiku, Gwamna Ifeanyi Okowa ya ce PDP za ta farfaɗo da fannin ilmi. Sannan ya nuna damuwar sa dangane da yadda ɗaliban jami’a su ka shafe watanni takwas a gida, ya na mai cewa ba za a samu irin haka a gwamnatin su ba.
Shi ma Gwamna Udom Emmanuel ya roƙi al’ummar Jihar Ondo su zaɓi Atiku, wanda ya ce shi kaɗai a cikin sauran ‘yan takarar zai iya haɗa kan Najeriya.
Shugaban jam’iyya Iyorchia Ayu da Babban Daraktan Kamfen, wato Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto, duk sun yi wa taron jawabai masu nuna fifikon Atiku kan sauran ‘yan takara.