Kasancewar wa’adin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bai wa dukkan jam’iyyun siyasa da za su shiga zaben 2023 su kammala mika sunayen gwanayen takararsu zuwa 9 ga watan Yunin 2022 ya cika a ranar Alhamis, jam’iyyun sun fitar da wadanda za su yi musu takara a matakai daban-daban na mulki, sai dai matakin da ya fi jan hankali shi ne na takarar shugaban kasa wanda za a gwabza a tsakanin jam’iyyun a ranar 25 g wata Fabrairun 2023.
Fito da nagartaccen dan takara kuma karbabbe ga al’ummar Nijeriya na da matukar muhimmaci idan har jam’iyya na fatan lashe zaben da za a gudanar, a kan haka ne muka tattaro ‘yan takarar da ake ganin taurarinsu za su fi haskawa a karon battar da za a yi a zaben na badi. Mun yi tsakure a kan wasu bayanan ‘yan takarar da irin ayyukan da suka yi a baya da kuma irin muradun da suke da su na kawo wa Nijeriya ci gaba da fafutukarsu ta kaiwa ga gaci.
Bola Ahmed Tinubu (APC)
A ranar Laraba 8 ga watan Yuni ne jagoran jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya sami nasarar lashe zaben zama can takarar shugabancin kasa na jam’iyya mai mulki ta APC a zaben da aka yi a filin Eagle Skuare da ke Abuja. Tinubu ya samu kuri’a 1,271 inda ya kayar da ‘yan takara 13 ciki har da tsohin Miistan Sufuri Rotimi Ameachi wanda ya samu kuri’a 316 da mataimakiih shugaban kasa Yemi Osinbajo, wanda ya tashi da kuri’a 235.
A hali yanzu dai an bude fagen fafatawa da sauran ‘yan takarar jam’iyyuan kasar nan a zaben da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu 2023 cikin ‘yan takarar akwai Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP wanda ake gani yana cikin na gaba gaba.
Nasarar da Tinubu ya samu ta faru ne bayan da wasu ‘yan takara 7 suka janye masa suka kuma nemi magiya bayansu su goyawwa Tinubu baya.
Bola Tinubu shaharraren dan siyasa ne a Nijetiya, ya yi gwamnan Jihar Legas daga shekarar 1999 zuwa 2007. Ya kuma tabazama wakili a majalsar wakilai a shekarar 1993. Tinubu ma’abucin rajin tabbatar da dimokradiyya ne da tabbatar da hadin kan kasa.
An haifi Bola Ahmed Adekunle Tinubu ne a ranar 29 ga watan Maris 1952 a Jihar Legas, ya yi karatun Firamare a ‘St. John’s Primary School’ Aroloya, Lagos ya kuma karatun sakandire a ‘Children’s Home School’ Ibadan ta Jihar Oyo, yana da mata mai suna Satana Oluremi Tinubu, wadda ke wakiltar Jijar Kegas a majaliusar Dattawa.
Tinubu ya tafi kasar Amurka don karatun digirinsa a shekarar 1975. Ya kamala karatun digirinsa a Jami’ar Jihar Chicago a shekarar 1979, a yayin zaman karatunsa a AMurka, Tinubu ya yi ayyuka da dama, kamar direba mota, aikin gadi da sauran kanana ayyuka don tallafa wa kansa da kudin kashe da dawainiyar karatunsa.
Bayan kammala karatunsa na jami’a da kyakyawar sakamako nan take wasu kamfanoni a kasar ta amurka kamar ‘Arthur Andersen, Arthur Young, Ernst and Whinney, Peat Marwick, Mitchell, Deloitte, IBM, Arthur Young, Deloitte, Haskins da kuma kamfanin Sells. A nan ne wani malamansa Farfesa a Jami’a ya shawarce shi ya zabi tsakanin kamfanin Deloitte da Touche saboda harkokinsu sun danganci bangaren albarkatin maid a iskar gas, wanda hakan kuma zai taimaka masa bayar da gudumwarsa ga Nijeriya.
Bayani ya nuna cewa, Bola Tinubu ya shiga harkokin suyasa ne a shekarar 1992 a karkashin jam’iyyar SDP. Yana tare dne da bangaren Shehu Musa Yar’Adua. Inda suke tare das u Dapo Sarumi, Abdullahi Aliyu Sumaila, Rabiu Kwankwaso da kuma Yomi Edu. Daga na kuma ya samu cin zaben majalisar dattawa mai wakilatar mazabar Legas ya yamma, inda ya rike mukamin shugaban kwamitin majalisa a kan kasafin kudi da harkokin banki.
Bayan soke zaben 12 ga watan Yuni na shekara 1993, elections, Tinubu, tare da wasu ‘yan siyasa sun shiga gwagwarmayar dawo da dimokradiyya a ta hanyar kafa kugiyar Democratic Coalition (NADECO). Tafiyarsa Gudun Hijira
Harkokinsa na NADECO baya yi wa shugaban mulkin soja na wannan lokacin ba (Sani Abacha). Don gudun musgunawa Tinubu ya yi gudun hijira zuwa kasar Benin daga nay a zarce kasar Birtaniya a shekarar 1994.
Bayan rasuwar Sani Abacha a shekara 1998. Sabin shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar ya sanar da jadawalin komawa turbar dimokradiyya, inda ya nemi Tinubu ya dawo daga gudun hujirar da yake yi a kasar Birtaniya, inda ya shga zabe ya kuma lashe kujerar gwamnan jihar Legas a karkashin jam’iyyar Alliance for Democracy Party (ADP) a watah Mayu na shekarar 1999. Gaggarumin ayyukan da ya na bunkasa jihar ya sanya aka sake zabensa karo na biyu ya kuma kamala wa’adinsa a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2007. Inda Babatunde Fashola ya gae shi.
Atiku Abubakar (PDP)
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ne ya lashe zaben da aka gudanar na fitar da dan takarar da zai yi wa jam’iyyar PDP takara a 2023, ya samu kuri’a 371 yayin da wanda yake biye dashi Gwamnan Jihar Raibas, ya tashi da kuri’a 237, an gudanar da zaben ne cikin tsatsaurar matakan tsaro a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja ranar Asabar 28 ga watan Mayu.
Cikin wadanda suka yi takara da Atiku akwai tsohon Shugaban majalisar dattawa, Dakta Bukola Saraki, wanda ya samu kuri’a 70 sai gwamnan Jihar Akwa Ibom Udom Emmanuel, ya zo na hudu da kuri’a 38. Sauran da suka yi takarar sun hada da tsohon shugaban majalisar dattawa, Anyim Pius Anyim, wanda ya samu kuri’a 14 sai gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya tashi da kuri’a 20.
Saura wadanda suka yi takarar sun kuma hada da tsohon Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose da Dele Momodu wanda basu samu ko kuri’a daya ba.
Wannan shi ne karo na biyar da Atiku ke samun nasarar zama dan takarar shugabancin Nijeriya, ya yi takarar a lokuttan baya a jam’iyyar APC da PDP.
A zaben da aka yi a shekarar 2019 ya yi takara a karkashin jam’iyyar PDP inda ya sha kaye a hannun Shugaba mai ci yanzu, Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC.
Tsohon mataimakin shugaban kasar zai fuskanci sauran ‘yan takara don neman kuri’ar ‘yan Nijeriya a zaben 2023.
A jawabinsa bayan an sanar da lashe zaben, Atiku ya mika godiyarsa ga dukkan ‘yan takara da ‘yan jam’iyyar a kan yadda suka bayar da hadin kai har aka samu nasarar gudanar da zaben a cikin nasara.
Ya kuma yi alkawarin farfado da tattalin arzkin kasar nan tare da kuma maganin mastalar tsaro da ake fuskanta a sassan kasar nan. Ya kuma nemi dukkan ‘yan jam’iyyar da suka shigar da karar jam’iyyar a kotuna daba-daban su janye a hada kai don a samu nasarar da ake bukata.
Rabi’u Musa Kwankwaso (NNPP)
Ita kuwa jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta sanar da cewa, Tsohon Gwamna Jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiya, Sanata Rabiu Kwankwaso, ne zai yi mata takarar shugabancin kasa a baban zaben 2023.
Shugaban jam’iyyar, Dakta Boniface Aniebonam, ya sanar da haka a taron manema labarai a Legas. Ya ce, Sanata Kwankwaso ne dan takara daya tilo da ya nuna bukatar tsayawa takarar.
Jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari za ta shiga takara da nufin maye gurbin jam’iyya APC a zaben da za a yi a shekarar 2023. Dama dai tuni ta ce APC da PDP dukka sun gaza saboda kowacce a ciki ta gwada irin salon mulkinta an gani ba tare da biya wa ‘Yan Nijeriya bukata ba.
Kolawale Abiola (PRP)
Ita kuwa jam’iyyar PRP a babban taron ta da ya gudanar a garin Kalaba ranar Lahadin da ta gaba sun zabi babban dan marigayi Chif MKO Abiola, Kolawole Abiola a matsayin wanda zai yi mata takarar shugabancin kasa a zaben na 2023.
Kola Abiola ya tashi da kuri’a 63 inda ya samu nasara a kan mutum 2 da suka shiga takarar tare dashi, wanda kuma ya hada da Patience Ndidi da Usman wandanda basu samu kuri’a ko daya ba.
Ana saran Kola ya fafata da sauran ‘yan takara daga sauran jam’iyyu a 2023.
Peter Umeadi (APGA)
Jam’iyyar All Progressibes Grand Alliance (APGA) ta tsayar da tsohon babban jojin Jihar Anambara, Peter Umeadi a matsayin wanda zai mata takarar shugabanci kasa a zaben 2023.
Mista Umeadi ya samu wannan nasarar ce a babban taron da jam’iyyar ta yi a hedikwatar jam’iyyar a babban birin tarayyar kasar nan, Abuja, inda wakilai masu zabe (Deliget) 150 suka tabbatar da zaben nasa ba tare da hamayya ba.
Mista Umeadi, wanda Farfesa ne a harkokin shari’a, ya yi ritaya ne a watan Maris na wannan shekarar ya kuma shiga jam’iyyar ne a karamar hukumarsa ta Anaocha da ke Jihar Anambara.
A jawabinsa na godiya bayan an ayyana shi a matsayin dan takarar jam’iyyar APGA, Mista Umeadi ya yi alkawarin samar da doka da oda da kuma ba bangarorin gudanarwa na mulki hakkokinsu, kuma zai gudanar da mulki ta hanyar tafiya da kowa da kowa.
Ya ce, ‘yan Nijeriya nada hakkin fuskantar rayuwa ta gari tare da more rayuwa kamar yadda ya kamata ya kuma yi alkawarin samar da tsaro a sasan kasar nan, ya yi tir da yadda ake kashe kashen rayukan al’umma a sassan kasar nan, ya ce dole kuma a farfado da dukkan bangarorin tattalin arzikin Nieriya.
Taron ya samu halartar ‘yan jam’iyyar da dama ciki har da Enyinaya Abaribe, Sanata mai wakiltar Abia ta yamma wanda ya sauya sheka zuwa jam’iyyar daga PDP kwanan nan kuma APGA ta bashi takara kai-tsaye.
Peter Obi (LP)
Tsohon Gwamnan Jihar Anambara, Mista Peter Obi na ya samu nasarar zama dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben da ke tafe na 2023.
Obi ya samun wannan nasarar ce bayan da dukkan wadanda suka sayi fom don takarar suka janye masa a taron da jam’iyyar ta yi a garin Asaba ta Jihar Delta.
Alhaji Usman Abdullahi, wanda ya jagoranci kwamitin gudanar da zaben ya bayyana cewa, ‘yan takara 5 aka tantance tare da amince dasu don tsayawa takarar, amma daga baya suka janye wa Peter Obi, ya kuma ce, wakilai masu zabe 104 suka samu halartar taron daga jihohi 36 har da Abuja babbar birnin tarayar kasar nan.
Amma ana cikin taron ne sai ‘yan takarar da suka hada da Farfesa Pat Utomi, Mista Joseph Faduri, Misis Olubusola Emmanuel-Tella da kuma Mista Charles Uchenna suka janye daga takarar abin daya ba Obi dammar lashe zaben ba tare da hamayya ba.
Daga karshe shugaban taron Abdullahi ya ayyana Obi, a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 96, inda ya samu nasarar shiga babban zaben shugaban kasa da za a gudanar a 2023. An kuma bayyana cewa, zaben ya gudana ba tare da wata matsala ba.
A jawabinsa bayan ayyana shi a mastayin wanda ya lashe zaben, Obi, ya ce, tabbas kasar nan na tsananin bukatar shugaba nagari da zai kai kasar ga tudun mun-tsira, ya yi alkawarin fitar da kasar nan daga dukkan matsalolin da take fuskanta wadanda suka hana kasar shiga sahun takwarorin ta a sassan duniya. Ya ce, hanya mafi sauki na yakar talauci a shi ne tsamar da al’umma daga kangin talaucin da suke fuskanta. Ya kuma bayyana cewa, gwamnatinsa za ta bayar da muhimmanci ga bunkasa harkar Ilimi, samar da wutar lantarki, da bunkasa tattalin arzikin kasa.
A kan haka ya nemi ‘yan Nijeriya su zabe shi a zaben da za a gudanar a shekara mai zuwa 2023. Hukumar zabe da jami’an tsaro sun samu halarartar taron an kuma gudanar ba tare da wata matsala ba.
Hamza Al-Mustapah (AA)
Jam’iyar Action Alliance (AA) ta zabi tsohon dogarin marigayi shugaba Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapah a matsayin wanda zai yi mata takara a zaben 2023. Ya kuma yi alkawin in har ya samu nasarar zama shugaban Nijeriya zai fuskanci kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi Nijeriya ta hanyar tarewa a dajin Sambisa.
Al-Mustapha ya kuma ce, zai kawo karshen kungiyar ‘yan ta’addan nan ta Boko Haram a cikin wattani shida.
Ya ce, jam’iyyasu ta AA za ta kawo karshe matsalar talauci da rashin aikin yi da zaran ta dare karagar mulkin Nijeriya, a kan haka ne ya nemi al’umma Nijeriya su kada musu kuri’asu a zaben da za a gudanar a 2023, ya ce, wannan gwamnati bata yi abin daya dace ba don saukaka wa al’umma radadin halin da suke cii na matsin tattalin arziki, ya nemi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta tabbatar da ta gudanar da sahihon zabe ba tare da magudi ba.
Omoyele Sowore (AAC)
Mawallafin jaridar nan ta intanet, ‘Sahara Reporters’ Omoyele Sowore ne ya samu nasarar shiga takara a babban zaben da za a gudanar a shekarar 2023 duk kuwa da cewa, ya samun irin wannan takarar a shekarar 2019 inda shugaba Buhari ya samu nasara a kan jami’iyyarsa ta AAC.
Sowore wanda ya yi suna a fafutukar kare hakkin biladam ya shiga jerin masu neman su gaji kujerar Muhammadu Buhari a matsayij shugaban Nijeriya.
A jawabinsa, ya yi alkawarin dawo da Nijeriya turbar da ta dace, tare da tsayuwa a kan kare hakkin ‘yan Nijeriya, ya yi korafi a kan yadda APC ke tafiyar da harkokin kasar nan, yana mai cewa, an danne wa al’umma hakkinsu an kuma hana su bayyana ra’ayinsu, ya ce, zai yi wa bangaren jami’an tsaro garanbawul ta yadda za su rage cin mutumcin mutane, zai kuma tabbatar da alkalai na yanke hukunci a kan lokaci don a rage cunkoson a gidajen yari, “Matasa na bukatar kulawa ta musammman, za mu samar da ayyukan yi ga matasa wanda ta haka ne yaki da ta’addanci zai samu cikaken nasarar da ake bukata”, In jI shi.
Prince Malik Ado-Ibrahim (YPP)
Shugaban kungiyar ‘Reset Nigeria Initiatibe’, Yarima Malik Ado-Ibrahim, ya samu nasarar zaman dan takara shugabancin kasa na jam’iyyar ‘Young Progressibes Party’, YPP.
Ya yi nasara ne da kuri’a 66 inda wadda take biye dashi Misis Ruby Issac ta samu kuri’a 4 a taron jam’iyyar da aka yi a Abuja ranar Laraba. Idan za a iya tunawa, matashin dan siyasa dan jam’iyyar APC Adamu Garba ne aka ba takarar tun da farko amma ya janye.
Bayani ya nuna cewa, an tantance masu kada kuri’a 74 amma mutum 70 suka kada kuri’ar su. A halin yanzu ana sa ran Yarima Ado-Ibrahim zai fafata da sauran ‘yan takara daga wasu jam’iyyun Nijerya don neman zama shugaban Nijeriya a shekarar 2023
Dumebi Kachikwu (ADC)
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta tsayar da Dumebi Kachikwu a mastayin wanda zai yi mata takara kujerar shugabancin Nijeriya a zaben shekarar 2023. A ranar Laraba 8 ga watan Yuni 2022 a babban taron jam’iyyar da aka yi a garin Abeokuta ta Jihar Ogun aka tabbatar masa da wannan nasarar.
Ya samu nasarar ne a kan dukkan ‘yan takarar da suka shiga zabe tare dashi, wadanda suka hada da tsohon mataimakin babban bankin Nijeriya Kingsley Moghalu.
“Dumebi Kachikwu ne sahihin dan takarar da zai iya kawo wa jam’iyyar mu cikakken nasarar da ake bukata,” in ji wata majiyar jam’iyyar.
A jawabinsa bayan an tabbatar masa da nasarar takarar, Kachikwu ya yi alkawarin jagorantar jam’iyyar zuwa samun nasarar da ake bukata, a kan haka ya nemi al’ummar Nijeriya su ba jam’iyyar goyon baya a zaben da za a gabatar a 2023.
Ya kuma nemi dukkan wadanda suka yi takara na kujeru daban-daban a jam’iyyar su kawar da son rai su hada kai don samun nasarar jam’iyyar a dukkan mataki.
“Da yardar Allah za mu samu nasara a 2023.” In ji shi.
Mista Yabagi Sani, (ADP)
Shugaban jam’iyyar ADP, Mista Yabagi Sani ya lashe takarar shugaban kasa na jam’iyyar a 2023.
Mista Sani wanda ya kasance shugaban jam’iyyar ADP ya zama dan takarar jam’iyyar ne ta hanyar masalaha da jam’iyyar ta gudanar a Abuja.
Da yake gabatar da jawabi, Mista Sani ya bayyana cewa jam’iyyar ADP za ta kasance mafita ga ‘yan Nijeriya wanda za ta hada kan maza da mata a wuri daya.
Ya kara da cewa Nijeriya kasa ce da ke dimbin arziki, amma an yi watsi da arzikin sakamakon rashin kyakkyawan shugabanci.
Ya sha alwashin cewa jam’iyyarsa za ta samar wa Nijeriya da ingantaccen shugabanci.