Indiya ta yanke shawarar rage kudin aikin hajjin 2023 da akalla Rufi dubu100, wato Rs 100,000.
Minista Smriti Irani, ne ya sanar da hakan a taron Hajjin Indiya da aka yi a New Delhi a ranar Asabar, 12 ga Nuwamba, 2022.
- Miji Ya Tsare Matarsa Na Tsawon Shekara Daya Ba Abinci A YobeÂ
- Sufeton ‘Yansanda Ya Ba Da Umarnin Tsaurara Tsaro A Hanyar Legas-IbadanÂ
Taron ya samu halartar mambobin Babban Kwamitin Hajji, tare da shugabannin kwamitocin alhazai na jihohi.
Hakan ya biyo bayan wani gagarumin zargi na cewa an kara kudin tafiyar Hajji daga Indiya a bara.
Tafiya zuwa Makkah ta karkashin Kwamitin Hajji na Indiya ta fi sauki a kan tafiya ta kamfanonin sufuri masu zaman kansu.
Kudaden aikin Hajjin 2022 a hakikanin gaskiya ya fi abin da masu gudanar da yawon bude ido ke karba, kamar yadda mahajjatan suka yi zargi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp