Babbar kotun tarayya da ke Jihar Kaduna, ta tabbatar da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Sanata Uba Sani a matsayin wanda zai tsaya takara a zaben 2023 a jihar.
Bayan dage sauraren karar har sau biyu kan karar da ke neman a soke Sanata Uba Sani a matsayin dan takarar gwamnan Jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar APC, kotun ta tabbatar da Uba Sani a matsayin wanda zai tsaya takarar jam’iyyar a zaben 2023.
- Me Zai Biyo Bayan Canza Wasu Kudade A Nijeriya?
- Ganduje Ya Gabatar Da N245.3bn A Matsayin Kasafin 2023 Ga Majalisar Dokokin Kano
Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, mai shari’a Mohammed Garba Umar, ya yi fatali da shari’ar da ta saba wa tanadin manufofin majalisar shari’a ta kasa.
Tun da farko Muhammad Sani Sha’aban ne ya doka Uba Sani a kotun, inda ya nemi kotun ta soke takararsa inda ya ce an yi zaben fidda gwanin ba bisa ka’ida ba.