• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2023: Kungiyar Afenifere Ta Yi Amai Ta Lashe

byYusuf Shuaibu
3 years ago
Lashe

Gamayyar kungiyar Yarbawa zalla ta Afenifere ta yi amai ta lashi, inda a baya ta bayyana cewa tana bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, saboda adalci, bin gaskiya da kuma rashin danne wani sashi na mika mulki ga yankin kudu maso gabasin Nijeriya, amma kuma a yanzu ta bayyana cewa tana goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyatr APC, Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023.

Shugabannin kungiyar Afenifere a dukkan fadin yankin kudu maso yamma ciki har da jihohin Kwara da Kogi sun suka bayyana goyan bayan a gidan shugaban kungiyar, Pa Reuben Fasonranti da ke Akure, Babban Birnin Jihar Ondo.

  • Ziyarar Da Shugabar Tanzaniya Za Ta Kawo Sin Za Ta Bunkasa Alaka Tsakanin Kasashen Biyu Zuwa Wani Sabon Matsayi
  • An Cafke Wasu Da Ake Zargi Da Hannu A Mutuwar Mutane Sama Da 130 A Indiya

Sun dai dauki wannan matakin ne bayan ganawa da Tinubu wanda ya ziyarci jihar domin gabatar da manufofinsa na sake fasalin Nijeriya.

Tinubu ya bayyana wa shugabannin Yarbawa cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin APC da ke arewa da sauran shugabannin yankin arewa sun yi Imani da cewa shi ne zai iya ceto Nijeriya daga kalubalan da ke fuskanta a halin yanzu.

Da yake gabatar wa shugabannin Yarbawan kundin manufofinsa na samar da ingantacciyar Nijeriya, Tinubu ya jaddada musu cewa za a samu ingantacciyar Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

Idan za a iya tunawa dai lokacin da ya ziyarci Pa Fasoranti a ranar 4 ga watan Maris na wannan shekara kafin zaben fid da gwani na jam’iyyar APC, Tinubu ya yi wa shugaban kungiyar Afenifere alkawarin cewa zai dawo a lokacin da ya samu tikitin takarar shugaban kasa.

Tinubu ya ce ya zo Ondo ne domin ya cika alkawarin da ya dauka a baya, inda ya bukaci shugabannin Yarbawan su gode wa Shugaba Buhari da gwamnonin arewa bisa ba shi dama a jam’iyyarn APC.

Tsohon gwamna Jihar Legas ya ce, “’Yan arewa sun tabbatar mun da cewa zan iya hada kan Nijeriya. Wasu sun yi kokarin zuwa wurin Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin gabatar da wani, amma shugaban ya ki amincewa da bukatarsu, inda ya dage sai an bi tsarin yadda dimokuradiyya ya shimfida. Shugaban ya ce duk wanda zai daga martabar jam’iyyar APC shi ne ya cancanta. Daga baya dai ya karkara zuwa ga gaskiya.

“Gwamnonin APC na arewa su suka dage dole sai mulki ya je yankin kudu, musamman ma kudu maso yamma. Gwamna Nasir El-Rufai da Abdullahi Ganduje da sauransu su suka goya min baya daga karshe,” in ji Tinubu.

Tun da farko dai, sakatare janar na kungiyar Afenifere, Cif Seinde Arogbofa ya bukaci Tinubu ya zama shugaban kasa domin hada kan Nijeriya da aiki tukuru wajen inganta kasa baki daya.

Ya ce, “Ba wai za ka kasance shugaban Yarbawa ba ne kadai, sai dai shugaban Nijeriya gaba daya. Lokacin da ka zama shugaban kasa, duk abin da za ka yi ka dunga tunawa da Nijeriya sannan kar ka manta da gida. Ka san irin bukatocinmu wadanda suka hada da samar da tsaro da inganta tattalin arziki. A yanzu haka kasarmu babu tsaro, muna bukatar ‘yansandan jihohi saboda tsaron kasarmu.”

Mataimakin gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa wanda shi ne ya tarbi Tinubu a madadin Gwamna Rotimi Akeredolu ya bayyana cewa, mutanen Jihar Ondo da kungiyar Afenifere suna goyon bayan Tinubu ya zama shugaban kasa.

Sakamakon ganawar kungiyar Afenifere da Tinubu, mai magana da yawun tawagar yakin neman zaben Atiku/Okowa, Daniel Bwala ya bayyana cewa kamata ya yi kungiyar Afenifere ta gayyaci sauran manyan ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 ba wai na APC kadai ba.

“Na yi tsammanin Afenifere za ta gayyaci manyan ‘yan takara guda hudu kamar yadda kungiyar arewa ta yi, amma sai ta gayyaci Tinubu kawai,” in ji shi.

Da yake mayar da martani game da goyon bayan Tinubu, Bwala ya ce kasancewa rashin halartar ganawar da wasu jiga-jigan ‘yan kungiyan kamar irinsu Pa Ayo Adebanjo da Cif Sola Ebiseni ya nuna goyon ba halattacce ba ne.

Bwala ya siffanta Tinubu a matsayin wanda yake kokarin amfani da kabilanci domin ya samu nasara.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi
Manyan Labarai

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki
Labarai

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu
Labarai

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Next Post
Masu Kudaden Haram Za Su Fuskanci Kalubale Da Sauya Fasalin Kudi —Buhari

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version