A daidai lokacin da ake fuskantar babban zaben 2023, gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya ajiye mataimakinsa, Injiniya Rauf Olaniyan, a matsayin abokin takara.
A maimakon hakan, nan take ya sauya shi da shugaban hukumar gidaje ta jihar, Barista Bayo Lawal, a matsayin abokin takara a 2023 na zaben gwamnan Jihar.
Lawal haifaffen Kishi ya fito daga karamar hukumar Irepo, ya kasance tsohon Antoni Janar na jihar Oyo wanda aka nada shi a 1999 a karkashin mulkin tsohon gwamnan Lam Adesina.
Gwamnan Jihar na yanzu Seyi Makinde ya nada Lawal a matsayin Shugaban hukumar gidaje na jihar Oyo.
Idan za ku iya tunawa dai an kwashe tsawon lokaci gwamna Seyi da mataimakinsa Engr. Rauf Olaniyan, ba sa ga maciji.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp