Yanzu dai kwanaki 9 kacal su ka rage a yi zaɓen shugaban ƙasa. Akwai muhimman batutuwa 10 da ya kamata a sani dangane da wannan zaɓe.
Mutum miliyan 93.5 su ka yi rajistar zaɓe. Sai dai ba lallai dukkan su ne za su yi zaɓe ba.
Zaɓen Nijeriya ya kai kwatankwacin zaɓen sauran ƙasashen Afrika ta Yamma baki ɗaya yawa, idan da a ce za su haɗu su yi zaɓe a rana ɗaya.
INEC ta buga ƙuri’u miliyan 187 don zaɓen shugaban ƙasa. Za a yi amfani da rabin su a lokacin zaɓen 25 ga Fabrairu. Idan ta kama sai an yi zaɓen raba-gardama, wato zagaye na biyu, sai a yi amfani da sauran rabin ƙuri’un kenan.
Jam’iyyu 18 ne su ka fitar da ‘yan takarar shugaban ƙasa a zaɓen ranar 25 ga Fabrairu.
Idan ta kama a yi zaɓen raba-gardama, wato zagaye na biyu yayin da zaɓen shugaban ƙasa bai fitar da wanda ya yi nasara ba, to INEC za ta shirya zaɓen a cikin kwanaki 21.
Idan kuma ba za a yi zaɓen raba-gardama ba, kuma wani ɗan takarar shugaban ƙasa bai kai ƙara kotu ba, to INEC za ta ƙone sauran ƙarin takardun zaɓe miliyan 93.5 da ta buga.
Akwai rumfunan zaɓe 176,846 da za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa. Amma yanzu sun koma 176, 606, saboda INEC ta sanar cewa ba za a yi zaɓe a rumfuna 240 cikin jihohi 28 da FCT Abuja ba.
9. Adadin ejan-ejan ɗin da Jam’iyyu 18 za su tura wurin zaɓe ya kai 1,642,386. A cikin su 1,574,301 ejan ne a rumfunan zaɓe, wato ‘polling egents’. Sai 68,088 kuma ejan-ejan ne masu sa-ido wurin tattara sakamakon zaɓe, wato ‘collation egents’.
Jihohin Taraba da Imo ne ke da mafi yawan rumfunan da ba za a yi zaɓe a cikin su ba. Yayin da Taraba ke da rumfuna 34, Jihar Imo kuwa har 38.
INEC ta ce ta rigaya ta bayar da katin shaidar ejan ga wakilan jam’iyyu a wurin zaɓe da wurin tattara sakamakon zaɓe. Saboda haka ba ta yarda mutum biyu su fito su ce jam’iyyya ɗaya su ke wakilta ba. Ejan ɗaya kaɗai INEC ta sani. Wanda ya yi karambani ko gangancin yi wa INEC shisshigi, za a damƙe shi ya fuskanci hukunci.