Wani Fasto a Mozambican ya mutu bayan da ya yi azumin kwanaki 40 a kokarinsa na yin koyi da Yesu Almasihu da aka nakalto a cikin littafin ‘Bible’ da aka ce ya yi azumi makamancin hakan.
Mamacin Francisco Barajah, fasto ne kuma wanda ya assasa cocin ‘Santa Trindade Evangelical’ a tsakiyar Manica, da aka tabbatar da mutuwarsa a ranar Laraba.
- Za A Rataye Wani Mutum Kan Kisan Wata Mata A Jigawa
- DSS Ta Gargadi ‘Yan Siyasa Da Yada Labaran Karya
An kwantar da shi a asibitin Beira lokacin da ke cikin mawuyacin hali da kokarin ceto shi.
A lokacin da ya kai kwanaki 25 yana azumi, ya rasa nauyi da kuzarinsa ta yadda har sai da aka kai gabar da ba ya iya tashi balle yin wanka ko tafiya.
Kwanaki kalila, ahlinsa da mabiyansa wato almajiransa sun daukeshi zuwa asibiti da kokarin ganin ya dawo cikin hayyacinsa amma haka bata cimma ruwa ba.
Mutuwar tasa ba ta bai wa almajiran cocinsa mamaki ko makwabtansa ba lura da yadda suka ga irin ramewa da tsomarewa da ya yi dukka sakamakon azumin da ya kama yi.