Yunkurin da magoya bayan jam’iyyun siyasa daban-daban ke yi na yin amfani da kafafen sada zumunta a matsayin fagen tallata masu gidajensu wajen jan hankalin jama’a domin ganin ’yan takarar da suke so sun yi nasara, ya tada kura tsakani dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da takwaransa na jam’iyyar Labour Party (LP) Peter Obi.
A cikin ‘yan watannin da suka gabata, kafafen sada zumunta sun shiga wani yanayi na tabarbarewar mahawara ta siyasa, inda magoya bayan ‘yan takarar shugaban kasa a kasar suka tsunduma cikin ayyukan yada rahotonnin karya da nufin bata sunayen ‘yan takara da nufin tayar da zaune tsaye.
A jiya ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Tinubu, ya bukaci takwaransa na Jam’iyyar Labour, Peter Obi da yaja kunnen magoya bayansa da da su daina yada kalaman karya da batanci ga dukkanin ‘yan takara.
Tinubu ya roki Obi da ya gaya wa magoya bayansa su daina yada karya da kuma tozarta shi da sauran ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Ya ce wasu ayyukan da ‘ya’yan kungiyar ‘Obedient’ suke yi a shafukan sada zumunta sun nuna cewa masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) da magoya bayan sa (Obi) duk abu daya ne.
Amma da yake mayar da martani ga Tinubu, Obi ya bayyana wannan Ikirarin na zargin cewa yana tare da IPOB a matsayin babban barna a yunkurin da jam’iyyar APC ke yi na danganta yakin neman zabensa da Biafra
Tinubu, wanda ya yi magana ta bakin daraktan yada labaransa da sadarwa, Bayo Onanuga, ya shawarci Obi da magoya bayansa da cewa, kamata yayi yakin neman zabe ya kasance kan al’amura, wanda zasu kawo ci gaba a rayuwa da kuma dorewar zaman lafiyar kasar nan.