Wakilai masu ikon zabe da suka fito daga shiyya shida na kasar nan a Jamiyyar PRP, sun zabi Dokta Sani Salhu Mustapha a matsayin dan takarar shugaban kasa a inuwar jamiyyar PRP a zaben shekarar 2023.
Deliget din Jam’iyyar PRP na bangaren marigayi tsohon shugaban jamiyyar na PRP kasa, Alhaji Balarabe Musa, wadanda ake yi wa lakabi da Gaskiya da Gaskiya ne suka gudanar da zaben a taron da suka yi a dakin taro na Arewa House da ke a jihar Kaduna.
- 2023: Gwarazan Jam’iyyu A Karon Battar Zaben Shugaban Kasa
- Burinmu Mata Da Matasa Su Fito A Dama Da Su A Harkokin Mulki Da Siyasa — CITAD
An bayyana Dokta Sani Salhu Mustapha a matsayin Wanda ya samu nasara ba tare da wata hamayya ba.
Shugaban jamiyyar na kasa tsagin Balarabe Musa, Alhaji Abdulmajid Yakubu Dauda ya sanar da cewa, “Taron ya amince da Dakta Sani a matsayin dan takarar Kujerar Shugaban a jamiyyar PRP”.
Yakubu ya kuma bayyana cewa, akwai Shari’a a gaban kotun da INEC da tsagin Falalu Bello kan zargin yunkurin wargaza jamiyyar”.
Abdulmajid ya ci gaba da da cewa, wannan yunkurin na wargaza PRP ba sabon abu bane, inda ya ce, kamar yadda kowa ya sani ne, an kafa PRP ne domin gwagwarmayar siyasa kuma duk wadanda suka yi yunkurin wargaza ta a baya, suma ba su samu nasara ba.
A nasa bangaren Shugaban jam’iyyar PRP na kasa, Dokta Falau Bello, ya ce, Kola Abiola dan Cif Moshood Abiola ne ya yi nasara a zaben fidda gwani na Jam’iyyar da aka gudanar da kuri’u 2097.
Kola ya doke babban abokin hamayyarsa, Alhaji Usman Bugaje wanda ya samu kuri’u 813 da Patience Ndidi da Gboluga Mosugu da suka kuri’u 329 da 263 bi da bi.
Falalu ya ce, an tattara sakamakon zaben ne daga jihohin da wakilan Jam’iyyar masu ikon zabe suka kada aka kuma mika su zuwa Abuja, inda sakamakon karshe da aka tattara a Sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja ya nuna wakilai 3522 ne aka tantance inda suka kada kuri’u 3416 an kuma samu guda 141 da suka lalace.
Tun da farko a nasa jawabin, Bello ya ce jam’iyyar ta yi zabukan fitar da gwaninta daban-daban a Jihohi domin tana son a kusantar da zaben ga al’uma.
Kola dai da ne ga marigayi Cif Moshood Abiola, mai taimakon jama’a kuma wanda ake kyautata zaton shi ne ya lashe zaben shugaban kasa a shekarar 1993 da gwamnatin mulkin soja ta Shugaba Ibrahim Babangida ta soke. Babban Abiola ya tsaya takara a jam’iyyar Social Democratic Party (SDP).