Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya samu nasarar lashe zaben fitar da gwani na jam’iyyar PDP na dan takarar gwamnan Bauchi da zai rike mata tuta a babban zaben 2023 da ke tafe.
Bala wanda ya samu nasarar biyo bayan sake zaben fitar da gwani da jam’iyyar ta yi a ranar Asabar sakamakon janyewar da dan takarar da ya lashe tikitin da farko Ibrahim Kasim Muhammad ya yi.
Bala ya samu nasara ne da kuri’u 646 da wakilan jam’iyyar suka kada, inda delegates 10 ba su halarci wajen zaben ba da ya gudana a dakin taro na otel din Zaranda.
Idan za ku iya tunawa dai Bala ya shiga a dama da shi a neman tikitin Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP amma ya fadi, inda Atiku Abubakar ya kayar da shi.
Da ya ke jawabinsa bayan ayyanashi a matsayin dan takara, Bala Muhammad ya gode wa sakataren Gwamnatin jihar Bauchi, Ibrahim Kassim Mohammed, bisa janyewa da ya yi a matsayin dan takarar jam’iyyar.
Bala ya ce, “Muna matukar godiya wa Allah Subhanahu Wata’ala. Ina godiya wa Iyalaina, da jam’iyyar PDP gami da al’ummar jihar Bauchi bisa damar da suka ba ni.
“Kamar yadda kuke sa ne, a kashin kaina na je neman shugaban kasa amma Allah bai bani nasara ba, amma a yau ina godiya ga dan uwana sakataren Gwamnatin jihar Bauchi da ya ga dacewar janye min domin na shiga a dama da ni takara a karo na biyu.”
Bala ya bada tabbacinsa na cigaba da yin aiki tukuru domin kyautata cigaban jihar Bauchi da al’ummarta a kowani lokaci. Ya kuma ce a shirye suke su fafata neman nasara a babban zaben 2023 da ke tafe.
Da ya ke ayyana sakamakon zaben, Baturen zaben, Murtala Damagun, ya bayyana cewa Bala Muhammad shine ya samu nasara a zaben Dan takarar gwamna da jam’iyyar ta gudanar, don haka ne ya ce shi ne zai yi wa PDP takara a babban zaben 2023 da ke tafe.