Rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP na iya ci gaba da tafiya kamar yadda gwamnan jihar Ribas kuma shugaban kungiyar gwamnoni ta G-5, Nyesom Ezenwo Wike, ya amince zai mara wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, tare da yin alkawarin samar da motocin yakin neman zabe ga dan takarar a jihar.
Sai dai ya sha alwashin ci gaba da zama a PDP domin yakar wadanda ya kira ” ‘yan fashi da makami” a jam’iyyar.
Hakan na zuwa ne yayin da Obi kuma ya fito fili ya watsar da dan takarar gwamnan jihar Rivers na jam’iyyar LP, Comrade Beatrice Itubo, ya marawa ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar PDP, Siminalaye Fubara, domin ya samu goyon bayan Wike kan burinsa na lashe zaben shugaban kasa a zabe mai zuwa.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, a kwanakin baya Wike da wasu gwamnoni hudu na jam’iyyar PDP da aka fi sani da G-5 sun fice daga taron yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar, saboda takun-saka tsakanin su da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.