ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2023: ‘Yan Damfara Sun Bude Manhajar Intanet Don Daukar Ma’aikatan Zabe – INEC

by Sulaiman
3 years ago
INEC

Wani gargaɗin baya-bayan nan daga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta ja kunnen jama’a cewa ba ta san da zaman wata manhajar da wasu ‘yan damfara su ka buɗe da sunan ɗaukar ma’aikatan zaɓe na wucin-gadi ba.

Sakataren Yaɗa Labaran INEC, Rotimi Oyekanmi ne ya yi wannan gargaɗin, ranar Talata a Abuja.

  • Kotu Ta Dakatar Da DSS Kan Cafke Shugaban Hukumar INEC

Ya ce tuni INEC ta rufe shafin manhajar ta na ɗaukar ma’aikatan zaɓe, kamar yadda ta yi bayani a baya.

ADVERTISEMENT

A cikin Satumba ne dai INEC ta yi sanarwar cewa za ta buɗe shafin manhajar a ranar 14 ga Satumba, 2022 ta rufe a ranar 14 ga Disamba, 2022.

“Wannan shafin manhaja na intanet, na bogi ne, ba na INEC ba ne. Saboda an rufe shafin manhajar INEC na ɗaukar ma’aikatan wucin-gadi, tun a ranar 14 ga Disamba, 2022.”

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Oyekanmi ya bayyana sunan manhajar ta bogi da: URL-http://www.yournewclaims.com/INEC/recruitment, cewa ta bogi ce kawai kuma a nesance ta.

A wani labarin kuma an samu tabbacin cewa akwai katin rajistar zaɓe har milyan 6.7 da har yanzu ba a karɓa ba a cikin wasu jihohi 17.

Rashin karɓar katin da aka yi rajista dai na ɗaya daga cikin abin da ke haifar da matsalar rashin zuwa a jefa ƙuri’a, kamar yadda INEC ta tabbatar cewa a zaɓen 2019 mutum miliyan 82 ne ke da rajistar zaɓe, amma mutum milyan 28.6 kaɗai su ka fita su ka jefa ƙuri’a.

Duk da yawan masu jefa ƙuri’a a Jihar Legas, waɗanda su ka yi zaɓe a jihar ba su cika miliyan biyu ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja
Manyan Labarai

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta
Manyan Labarai

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka
Ra'ayi Riga

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Next Post
2023: Mai Binciken Kudin PDP Da Wasu Jiga-jigan Jam’iyyar Sun Koma NNPP A Gombe

2023: Mai Binciken Kudin PDP Da Wasu Jiga-jigan Jam'iyyar Sun Koma NNPP A Gombe

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.