An bukaci Jam’iyyar APC da ta tsayar da dan takarar shugaban kasa wanda zai iya cimma irin nasarorin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya samu.
Kwararren masanin harkokin yada labari, Olumide Lawal, ne ya yi wannan kiran ga masu ikon jefa kuri’a a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar mai zuwa.
- Babu wata Yarjejeniya Da Aka Gindaya Cewa Za A Ba Tinubu Shugaban Kasa Bayan Buhari -Yerima
- Kwamitin tantance ‘Yan Takarar Shugaban Kasa Na APC Ya Yi Watsi Da ‘Yan Takara 10 Cikin 23
Ya kuma kara da cewa, daya daga cikin masu neman kujerar da ya dace da da wannan bukatar shi ne, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Ahmed Sani Yarima.
Lawal ya ce tun a shekarar 2006, ya aike da sakon cewa, Yarima yana kudurin bunkasa kasuwanci da “samar da shugabanci nagari mai cike da kishin kasa da magance matsalolin kasar ta fuskoki da yawa.”
Lawal ya ci gaba da cewa, “Yarima ya kasance mutum ne mai kishin kasa, ya dogara kacokan akan kyakkyawar niyya da yake da ita tsawon shekaru.
“Yana da kyakkyawar mu’amala tare da sauran masu takara. Idan aka yi la’akari da cewa APC jam’iyya ce mai gaskiya, ba za a samu matsala ba ga Yariman idan ya fito a karkashin irin wannan tsari na zaben fidda gwani na gaskiya da adalci.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp